Ticker

6/recent/ticker-posts

Noma Yakin ‘Yan Arewa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Noma Yaƙin ‘Yan Arewa

Wannan mawaƙin ya yi wannan waƙar ne da ta ƙasaita domin ya nuna irin muhimmancin sana’ar noma, da kuma nuna irin matsayin noma ga mutanen Arewacin ƙasar Nijeriya. Ita ma ba wani manomi ne ya yi wa ita ba, amma ya yi ta ne don noma.

 

Ga yadda waƙar take kamar haka:

 

 G/Waƙa: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

.  ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Babbar sana’ar mutanen Arewa.

  ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Kai kun ga Mamman Shata na Yelwa

: Ko ni ma Noma nike yi,

  ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: In na yi yawo[1], nai waƙe-waƙe,

: Na dawo gidana,

: In na zauna gona zan je in riƙe ta.

  ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Noma sana’ar Ɗan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

Jagora: Saye da sayarwa, ‘yan kasuwaci,

: Noma shi ab babbar sana’a,

: Kun san shi noma ginshiƙi[2] ne,

: Shi ne gadon ‘yan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Manyanmu kowa noma yake yi,

: Bare mu ƙanana mu kama mu duƙa,

: Babbas sana’ar mutanen Arewa,

: Noma gadon Ɗan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Ku bar ragganci ‘yan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin[3] ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Kuna ji fa manyanmu na gargaɗinmu,x2

: A garje kowa ya zan kama aikin shi,

: Noma aikin ‘yan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Zama kan hakan nan ba aikin komai,

: Bai zai jawo alher ba,

: Noma shi ne ‘Yan Arewa.

  ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Ka ga ƙato ya yi zaune ga titi

: Sai annashuwa, yana doka sawu,

: Sai dariya ƙyalƙyatawa a titi,

: Wannan ba aiki ne ba yara,

: Ya duƙa ga aiki koko sana’a,

: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

. ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

 Jagora: Duka da sawu da duka da hannu.

: Sara da adda, da dukan takobi,

: Wannan ai ba yaƙi ba ne ba,x2

: Yaƙi a zuci shi ne yaƙi,

: Ku garje kowa ya ɗau sana’a,

: In ba sana’a ta hannu zuwa ka,

: Koma gona ka zan kama aikinka,

: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

Jagora: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

Jagora: Ku duba ga Shata Muhamman na Yelwa,

: In ya yi yawonsa yai waƙe-waƙe,

: Na zaga dud duniya na yi waƙa,

: Na komo gidana na zauna na huta,

: An ce da kai damina ce ta fadi,x2

: Gonata zani in kama gyara,

: In shuka kana in kama noma,

: In maimai kana in kama huɗa,

: In n agama amfani na gyara,

: Na kai gidana na kimtsa na ɓoye,

: Kannan in fice in ɗau waƙe-waƙe,

: Noma gadon ‘Yan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

Jagora: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

 

Jagora: Noma aikin ‘Yan Arewa

‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.

Jagora: Da mai teburi shi da mai saida goro,

: Da mai ɗauka ba ka yana saida taba,

: Da mai kanti, har zuwa mai sawowa,

: Ya zo nan ya saida a ce ya ci riba,

: Noma shi kam ginshiƙi ne.

  ‘Y/ Amshi: Noma yaƙin ‘Yan Arewa.[1]  Tafiye-tafiyen da yake yi wajen ziyarar iyayen gidansa ya yi masu waƙa.

[2]  Babbar hanyar neman abinci ce wadda kusan ta fi kowace hanya.

[3]  Babban abin da aka runguma gadangadan.

Post a Comment

0 Comments