Ticker

6/recent/ticker-posts

Gaishe ku Manoman Arewa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Gaishe ku Manoman Arewa

Wannan waƙar ba wani mutun ya yiwa ita ba sai dai jama’a ya yi wa waƙar saboda noman da suke yi. Dubi yadda yak eta cewa a cikin waƙar:

 G/Waƙa: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: Gaishe ku manoman Arewa.

. ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: A gaishe ku manoman Arewa.

 ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: A gaishe ku manoman ƙasammu.

: A gaishe ku manoman Arewa.

 ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

Jagora: A gaishe ku manoman jihammu

: A gaishe ku manoman Arewa.

 ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

Jagora: Mu dai ‘yan lardin Arewa.

: Mu dai bakin ƙasar Arewa,

: Kowace sana’a mun iya ta,

: Amma fa manoma ne mu ma,

: A gaishe ku manoman Arewa.

  ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: Idan ka ga mutum ya yi zaune,

: Babbar riga[1] tana wuyanai,

: Babbar taguwa tana wuyanai

: Babban wando yana ƙafatai,

: Sai ya zama babban manomi.

  ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: Na zaga ƙauyukan Arewa,

: In nag a mutun ya yi biki,

: Ya sa riga ya sa wando,

: Babbar riga tana wuyanai,

: Ga agogo yana hannunai,

: Ga gilashi yana idonai,

: Ga doki ɗandubu yah au,

: To ya zama babban manomi.

 ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: Han nai sha’awa, na yi zaune,

: Sai na zama babban manomi.

  ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: A gaishe ku manoma na birni,

: A gaishe ku manoma na ƙauye,

: Da kowane manomin Arewa.

 ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

 Jagora: Idan na shiga roƙon manoma,

: Ni hau wani daɗi nike ji,

: Noma shiga Dodon Arewa.

  ‘Y/ Amshi: A gaishe ku manoman Arewa.

 

3.1.4  Gonar Jori

Ita kuma wannan waƙar Shata gona ce ya waƙe, wato gonar Jori Hammani tsohon shugaban ƙasar Nijer. Ba kaitsaye mai gonar ne ya yi wa waƙar ba, a a, ya dubi yadda gonar take ne domin ya sanar da jama’ar irin yadda ta ƙayatar da shi.

 

 

Ga yadda waƙar take kamar haka:

 

 G/Waƙa: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

Jagora: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

:Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba,

: Zaman an kai ni gonar Jori.

 ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Waje ɗaya ga wurin yin[2] gero,

: Waje ɗaya ga wurin yin dawa,

: Waje ɗaya ga wurin alkama nan,

: Waje ɗaya ga wurin shinkafa,

: Ni an kai ni gonaj Jori.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: A nan kuma ga tumaki,

: Ta nan kuma na ga shanu

: Ta nan kuma ga dawaki hertat,

: Kana na ga garken ɓauna,

: Sadda na taka gonaj Jori.

 ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Gabas da Arewa gandun sarki,x2

: Gusun hay Yamma gandun sarki,

: Ama ka tashi gonaj Jori.

 ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Afirika duk cikar faɗinta,

: Gona dai mutum zai shirya,

: Bat a kai ga gonar Jori.

 ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Zaman an kai ni bakin gona,

: Na duba Gabas ba iyaka,

: Na yi Arewa nan ba iyaka,

: Nai nan Yammaci ba iyaka,

: Na duba Kudu ba iyaka,

: Na abu abin mamaki,

: Don na taka gonaj Jori,

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Ni na je Yamai na ji daɗi,

: Ni na je Yamai nai kallo,

: Bayan na ga Jori da Aisha,

: Har aka kai ni gona kallo.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Ga kwakwa ta ci an shuka,

: Ga kwakwa ta manja jere,

: Ga ayaba abarba jere,

: Ga kwakwa abar kallo nai,

: Ni an kai ni gona kallo.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

Jagora: Nan kuma rijiyar kifi ne,

: Kai kallonka Shata ka zo

  ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Ga inibi abincin Turai,

: In an kai ka gonaj Jori.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Kai komi kake so ga shi,

: Komi kai tunani ga shi,

: Rannan na gano mamaki,

: In an kai ni gonar Jori.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Na gode wa sarkin baƙi

: Isah Bube sarkin baƙi,

: Shi ya kai ni gona kallo.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Ka ji kiɗin manoma mun yi,x2

: In an kai mu gonaj Jori.

 ‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Shi kuma Jori ɗan Hammani,

: Bayan shugabancin ƙasa duka,

: Ni na ba ka sarkin noma.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Kai da dai aka kai ni gonaj Jori,

: Nad duƙa abin da nike so,

: Nis same shi gona gashi,

: Na yi kirari, nai addu’a duk,

: Bayan shugabanci ƙasa duka,

: Han na bashi sarkin noma.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Shi ke shugabancin ƙasa duka

: Ni kuma na yi sarkin noma,

: Shi nak kai wa sarkin noma.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.

 

Jagora: Afirika duk cikat ta da faɗi,

: Wadda idan ka duba kwata[3],

: Gonatai a duba a gan ta,

: Ba mai tsere gonaj Jori.

‘Y/ Amshi: Kowaj je Yamai yai kallo,

: Wannan bai kamar Shata ba.



[1]  Malummalum.

[2]  Wurin da ake shuka.

[3]  Bakiɗaya.

Post a Comment

0 Comments