Gidan Gona Dabiran

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Gidan Gona Dabiran

    Wannan waƙar da Shata ya yi ba wani manomi ne ya yi wa ita ba, amma ya yi wa gidan gona ne na ubangidansa Sarkin Daura saboda burge shi da ya yi a kan kayayyakin amfanin gona da ke tattare a gidan gonar. Ga yadda waƙar take kamar haka:

     

    G/Waƙa: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Za ni gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ka ji kiÉ—i ya koma Daura,

    : Har a gidan gona Dabiran,

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Na tafi gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Babu zaman banza Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Asharari baya zama Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

      Jagora: Kuma raggo baya zama Dabiran

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

      Jagora: Kun ji fa can lungun Dabiran,

    :Raggo baya zama Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ba a lalaci Dabiran.

    ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ba a sakarci Dabiran

    ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kullun sai kai aiki jajir

    ‘Y/ Amshi : Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora : Ko ni nan da je Dabiran

    : Na ɗau waƙa han na fara,

    : Sai sarki y ace bari shata,

    : Sai ka je aiki Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Tsarci ka zauna tafi riÆ™i galma,

    : Hay yaran Shata Dabiran

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Nai noma kuma nai ‘yah huÉ—a

    : Nai kimtsin taki nai gyara,

    : Na komo nan in waƙata,

    : A nan gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Za ni gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Muka ga gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Na je sarÆ™ahi kallon gona,

    : To malam kai ma sai ka yi,

    : Idan dai hak ka zo Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Ta ko ta ina aiki Dabiran

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Nai Yamma gona Dabiran,

    : Na yi Gabas gona Dabiran,

    : Arewa ma gona Dabiran,

    : Na yi Hamada gandun sarki,

    : In ka je gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ko’ina iya kallonka,

    : Duk sararin gona Dabiran

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ka yo Yamma kaÉ—an ga gulbi,

    : Nan ka gabas duk babu iyaka

    : Duk a cikin gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Noma daga Daura sai Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Ku bar mana ƙaryar aiki dangi,

    : Na gano noma tsabatai,

    : Ran da na je kallo Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Ranad da na je kallo Dabiran

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Ga sarki ga dangin sarki,

    : Noman hannu yana Dabiran,

    : Noman injin na Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Noman injin na Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Shata mu yi aiki Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ba a ashararu cikin Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ba a shashanci nan Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Wurin noman rani gashi daban

    : Wurin noman damina gashi daban

    : Malam in ka je Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Gonam mai gayya Dabiran.x2

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.x2

     

    Jagora: Zani gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Alheri nema Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Ya Allah bar mani mai gayya,

    : Allah kumabam man Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ya Allah bam mani Maigayya

    : Bam mani kuma gonad Dabian.

      ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kai mai Æ™arhi ga Dabiran.x2

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.x2

     

     Jagora: Alheri gonad Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Wannan lambu ya kai lambu

    : In ka je gonad Dabiran.

      ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

      Jagora: Ga wani lambu ca DPO

    : Gawurtacce ƙasaitacce

    : In kaj je can fegin Daura.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Babu zaman banza Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kai ka san noma na Daura.

    : Balle in ka je Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.x2

     

    Jagora: In dai zancen noma zakai.

    : Ni na san noma na Daura,

    : Balle in ka je Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Yaro in ka je Dabiran,

    : Kai kallo kallon ya ishe ka.

    : Zo nan kuma mu je DPO

    : Ka ga babban lambun DPO

    : Wannan duk a gidan na zaune.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Za ni gidan gona Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

    Jagora: Tarihin noma na Daura.

    : Kai ilimin noma na Daura.

    : Sanin aikin noma na Daura,

    : Yaro in ka je Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     Jagora: Waje É—aya ga gautan Turawa.

      ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Gauta namu yana nan daje

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kana ga mangwaro Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kana ga gwaba Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kai yara ga ilmi Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kana ga yalo Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Ga wani irin tattasai nan,

    : Manya kana bashi da yaji,

    : Ci ma zakai É—anye nai,

    : Muddin in ka je Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Kana ga É“auren Turawa.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Rani da damina aiki ne

    : Ga alkama gonad Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Sannan ka gan ta iya kallonka,

    : Ga alkama gonad Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

     

     Jagora: Yaro kai ka san Dabiran.

     ‘Y/ Amshi: Za ni gidan gona Dabiran.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.