Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Noma Babbas Sana’a
Ita wannan waƙa
ya yi ta don noma nei, ya yi kira ga jama’a don su dawo ga sana’ar noma, an
lura cewa a lokacin da ya yi waƙar mutane sun fara kauce wa sana’ar
noma ne suna yin wasu sana’o’i, kamar hada-hadar man fetur da kwangiloli da
saurnsu, sai Gwamnati ta umurci mawaƙa a lokacin da su
juyo da hankulan jama’a wajen sana’ar noma, nan ne fa sai gogan naka ya yi
wannan waƙar.
G/Waƙa:
Noma babbar sana’a,
:
Koway yi ta ya bar rasawa.
Jagora: Kowa tsare noma daidai ne,
:
Kowa aje gero da dawa,
:
Wannan ya ɗebe takaici.
‘Y/
Amshi:
Noma babbar sana’a,
:
Kowa ya yi yabar rasawa.
Jagora: Ka taimaki bayinka Allah,
:
Allah shi ne mai iyawa,
:
Ka taimaki bayin Allah,
:
Allah shi ne mai iyawa.
‘Y/
Amshi:
Noma babbar sana’a,
:
Kowa ya yi ta ya bar rasawa.
Jagora: Can dori Nijeriya ƙasarmu,
:
Allah ya bada arzikin noma,
:
Mu noma gero mu noma dawa,
:
Ga shinkafa ga gyaɗa,
:
Ga auduga muna noma,
:
Ga masara kuma ga shinkafa,
:
Ga acca kuma ga alkama muna noma,
:
Arzikin man fetur ya motsa,
:
Kasuwar man fetur ta katce,
:
Munka watsar da noma,
:
Munka koma a kan kwangiloli,
:
Ga shi arzikin fetur ya ƙare ƙasar nan,
:
Can ƙasashen da muke kaiwa,
:
Kasuwar mai ta faɗi!
:
To ‘yan Nageiriya yanzu me zamu komawa,
:
Ƙara
mu koma kan noma,
:
Ƙara
mu koma kan noma,
:
Mu tara abinci kasarmu,
:
Mu samu abinci da zamu ci,
:
Mu samu abinci sutura kana mu,
:
Nemi kuɗi mu kare mutuncin
na kanmu,
:
Mu kare mutuncin ƙasar ga,
‘Y/
Amshi:
Mu kare mutunci na kanmu,
:
Mu kare mutuncin ƙasar ga.
Jagora: Kun san gero da dawa,
:
Da sauran abunda za mu ci,
:
Shi muka ci Najeriya, amma
:
Auduga da gyaɗa to ita ce zamu ɗauka,
:
Mu kai ta can ƙasashen waje,
:
Mu sayar mu samo kuɗɗi,
‘Y/
Amshi:
Mu kare mutuncin ƙasar ga
Jagora: In mun samo kuɗi masu amfani,
:
Kana mu gina masu amfani,
:
Kayan amfanin gona ko’ina a kai,
:
Mu kare mutuncin na kammu,
‘Y/
Amshi:
Mu kare mutuncin ƙasarga
:
Indai mun samu kuɗi da yawa,
:
Ƙara
mu je mu nemi ilimi,
:
Mu kai ‘ya’yanmu su smu ilimi,
:
Mu kare mutuncinmu na kanmu,
Jagora: Mu kare mutuncin ƙasarga,
:
Kowa ya kare mutuncin na ƙasarga.
:
Ya ƙare mutuncin na kainai,
:
Ya kare mutuncin ƙasarga,
:
Noma babbar sana’a,
Jagora: Wadaduk nikaso Najeriya,
:
Mutane dun na hore ku,
:
Manyan garuruwanmu,
:
Kowane gari kazo,
:
Kai hangi dala ta gyaɗa,
:
Ka hangi dala ta auduga,
:
Kowane gaya mun tara,
:
Indai mun miƙa mun yi ƙwazo,
‘Y/
Amshi:
Mun kare mutuncin ƙasarga.
Jagora: Mun kare mutunci na kanmu,
‘Y/
Amshi:
Mun kare mutuncin ƙasarga.
Jagora: Darajar naira mu da ta faɗi,
‘Y/
Amshi:
To kuma sannan zata dawo.
Jagora: Darajar naira mu data ta faɗi,
‘Y/
Amshi:
To kuma sannan zata dawo.
Jagora: To kuma sannan ku ma’aikatan
Najeriya,
:
To ku tsaya a kan gaskiya,
:
Kowa ya tsaya Allah,
:
Kai ta tsaya ga naka aiki,
:
Ni in tsaya ga nawa aiki,
:
In mun yi hakan mu taimaki kanmu,
:
Kar mu tsaya muna yin ƙeta,
:
Muna cutar kanmu da kanmu,
:
Kai babba ka shirga ɓarna,
:
Sannan ka ce yaronka bai yi,
:
Kowa duk ya tsaya ya dage,
:
Mu kare mutuncinmu zak kyau,
‘Y/
Amshi:
Mu kare mutuncin mu kaz kyau,
:
Mu kare mutuncin ƙasarga,
:
Noma babbar sana’a rasa ba,
:
Kowa yita ya bar rasawa.
Jagora: Kai/ku jama’a Najeriya,
:
Talakawa da sarakuna,
:
Da ku ma’aikatan gwamnati,
:
Alhji Musa Ɗan kwairo,
:
Shi ma ya yi horon jama’a kowa,
:
Ya kama noma da gaskiya,
:
Ni ma Alhaji Musa Ɗankwairo,
:
Bayan na aje kotsonnina,
:
Na je Sakkwato can gidana,
:
Ni ma zan koma gona,
:
In kama noma ƙwarai da gaske,
:
Ina tara gero, in tara dawa,
‘Y/
Amshi:
In nemi abinci na kaina,
:
In nemi abinci na kaina.
Jagora: Na kare mutuncin na kaina,
‘Y/
Amshi:
Na kare mutuncin kasarga.
:
Noma babbar sana’a,
Jagora: Kowa ya tsaya ya yi aiki,
‘Y/
Amshi:
Yawon banza ba’ason nai.
:
Noma babba sana’a,
Jagora: Da ku ma’aikatan gwanmen,
:
Da manya-manyan sarakunanmu,
:
Kowa ya bada goyon baya,
:
Mu taru mu ceto ƙasar ga.
‘Y/
Amshi:
Mutaru mu ceto ƙasar ga,
:Jama’a
mu taru mu ceto ƙasar ga.
:
Noma babba sana’a,
Jagora: Kowa ya kama aikin daji,
:
Kowa naz zan baida aiki,
:
Ya zo ya ɗauki fartanya,
:
In yay yi hakan ya yi dai-dai.
‘Y/
Amshi:
In yay yi hakanga ya yi dai-dai,
:
In yay yi hakanga ya yi dai-dai.
Jagora: Kowa naz zan baida aiki,
:
Yana yawo ga titi ga banza,
:
Irinsu ka yan sace-sace.
‘Y/
Amshi:
Irinsu ka yan sace-sace,
:
Noma babbar sana’a,
:
Kowa ya yi ta yabar rasawa.
Jagora: Ka taimaki bayinka Allah,
‘Y/
Amshi:
Allah kai am mai iyawa.
:
Noma babba sana’a.
Jagora: Manyan sojojin Najeriya,
:
Sun ce kowa ya koma noma,
:
In kun yi hakan kun yi…
‘Y/
Amshi:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
Jagora: Manyan ‘yan sanda Nijeriya,
:
Kowa ya koma noma Ƙwairo,
:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
‘Y/
Amshi:
In kun yi hakan kun yi dai dai.
Jagora: Manyan kwastam na Najeriya,
:
Kowa ya koma noma Ƙwairo,
:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
‘Y/
Amshi:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
Jagora: Imagireshin da N.S.O ,
:
Kowa ya kama noma nai,
:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
‘Y/
Amshi:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
Jagora: Sarakunanmu na najeriya,
:
Kowa ya kama noma nai Ƙwairo,
‘Y/
Amshi:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
Jagora: ‘Yan kasuwa na najeriya,
:
Kowa ya kama noma Musa,
‘Y/
Amshi:
In kun yi hakan kun yi dai-dai.
:
Noma babbar san’a,
Jakora: In kun yi hakan kun yi dai-dai,
:
Noma babbar sana’a,
:
Sai mun aje gero mun aje dawa,
:
Ga masara ga alkama,
:
Ga Shinkafa ga masara,
:
Idan abinci ya taru,
‘Y/
Amshi:
Sannan darajar naira za ta dawo,
:
Sannan darajar naira zata gyaru,
:
Noma babbar sana’a.
Jagora: Mun shirya muntara aiki,
:
Ga ya nan ya barmu jibje,
:
To ku yan najiriya ƙara,
:
Mu motsa mu miƙe,
:
Mu kare mutuncinmu ya fi.
‘Y/
Amshi:
Mu kare mutuncin ƙasarga,
Jagora: Kaɗa da abincin ƙasarmu,
:
Mun san mun samu komai,
:
Allah ya albarkato ƙasar,
:
Najeriya da arziki sai in,
:
Mun ƙi yin biɗa in mun miƙe,
:
Mun nemi na kanmu,
:
Allah za ya taimake mu,
:
Kowa kan nemi taimako,
:
Gun Allah sai ya yi mai,
:
Diba min faɗin Najeriya,
:
Ko’ina akwai magurzayye,
:
Na gurzar auduga,
:
Sannan Najeriya akwai dala ta gyaɗa,
:
Sannan akwai dalan auduga,
:
To diba yanzu babu ko guda,
:
Kama aiki Mu kare mutuncin ƙasarmu,
‘Y/
Amshi:
Mu kare mutuncin na kanmu.
Jagora: In mun yi hakan,
‘Y/
Amshi:
Mun yi dai-dai,
Jagora: Yawon banza ba a so nai,
‘Y/
Amshi:
Yawon banza ba a so nai,
Jagora: Aiki a yi domin Allah,
:
Ba na bari domin Allah,
‘Y/
Amshi:
In mun yi hakan dai-dai,
Jagora: A kama hanyoyin sana’a,
:
Sannan shara’a a kan gaskiya,
:
In dai mutum na nashi aiki,
:
To ka bar shi da na shi aiki,
:
Ke ma ki bari in yi nawa,
‘Y/
Amshi:
Ke ma ki bari in yi nawa,
Jagora: Ko’ina ka bari in yi nawa ,
:
In mun yi hakan mun yi dai-dai,
:
In mun yi hakan mun yi dai-dai,
‘Y/
Amshi:
Noma babbar sana’a,
Jagora: Abin da a kyawo garemu,
:
Mu daina shawar kayan waɗansu,
:
Mu daina shawar kayan waɗansu,
:
Mun dinga shawar kayan ƙasarmu,
:
In mun hakan.
‘Y/
Amshi:
Mun yi dai-dai.
:
In mun hakan mun yi dai-dai.
Jagora: Abin da ak kyawo garemu mu
daina,
:
Shawar kayan waɗansu,
:
Mu dinga shawar kayan ƙasarmu,
:
In mun yi hakan,
‘Y/
Amshi:
Mun yi dai-dai.
Jagora: Jama’a in mun yi hakan.
‘Y/
Amshi:
Mun yi dai-dai,
:
Noma babbar sana’a.
Jagora: Malam ka ce gyara ka kai,
:
Wai kai dan kona da mulki,
:
Koko don kana da arziki,
:
Ka je ka sawo,
:
Kayan ƙasashen waje,
:
Don ka sayar, a ƙi sayen,
:
Wa gidanka ka/kai kuɗi ka kai su,
:
Can waje, kabar gida ba komi,
:
To wai kai don ka waye, to shiko,
:
Talakawa in sun zo sai ku ce sun yi,
:
Laifi sai in kun kare mutuncin ku,
:
Sai su ma sun yi ƙi yi,
:
Su kare mutuncin ƙasar ga.
‘Y/
Amshi:
Su kare mutuncin ƙasar ga.
:
Noma babbar sana’a koway yi ta,
:
Noma babbar sana’a koway yi ta,
Jagora: Koway yi gyara ya hi ɓanna[1],
:
Gwamnati na horon jama’a,
:
Kowa ya kama aiki da gaske,
:
Kowa naz zan Bai da aiki,
:
Wannan ya cuci ƙasa,
:
Sannan kuma ya cuci kainai,
‘Y/
Amshi:
Sannan kuma ya cuci kainai,
:
Noma babbar sana’a,
:
Koway yi ta ya bar rasawa.
Jagora: Dan ƙwairo
na sha dariya,
:
Na iske Bahillace daji,
:
Yana ta kiwon Shanu nai,
:
An ba shi hurar gero ya sha,
:
Dan nan sai yac ce “miyetti”[2],
:
Garɗi ne yar ratci
kainai,
‘Y/
Amshi:
Garɗi ne ya ratci
kainai,
:
Noma babbar sana’a,
:
Kowa yi ta ya bar rasawa.
Jagora: Ka taimaki bayinka Allah.
‘Y/
Amshi:
Allah kai am mai iyawa,
:
Noma babbas sana’a,
:
Koway yi ta ya bar rasawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.