Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Waƙoƙin Noma Na Alhaji Musa Ɗan’ba’u Gidan Buwai
An haifi Musa Ɗanba’u a shekarar 1957 a wani ƙauye da ake kira Gidan Buwai, wanda ke a ƙaramar hukumar mulkin Raɓah ta cikin jihar Sakkwato. Ya tashi a wannan garin nasu ne na Gidan Buwai har zuwa girmansa a ƙarƙashin kulawar mahaifinsa mai suna Abu Mai ɗan jaki. Ya yi karatun muhammadiyya gwargwadon hali tun yana ɗan ƙarami.
Mahaifinsa
wato Abu Mai ɗan jaki makaɗin goge ne, don
haka muke iya cewa ya gaji kiɗa da waƙa ne gareshi. Ya fara kiɗa da waƙa
tun a lokacin da yana ɗan saurayi. Da
farko ya fara da kiɗan kokowa/kokawa
har zuwa ƙarshe-ƙarshen shekarar 1970, inda ya gwama
kiɗin da kiɗin sauran jama’a da
kuma kiɗe-ɗiɗen siyasa da na
sarauta. Wannan harkar ta kiɗin ya cigaba da ita har zuwa ƙarshen
rayursa.
Kusan duk garuruwan ƙasar Hausa babu inda bai sa ƙafarsa ba wajen waƙa, kuma ya yi wa kowa da kowa waƙa tun daga malamai da sarakai har ‘yan siyasa. Hasali ma tauraruwarsa ta fara haskawa ne a lokacin siyasar jamhuriya ta biyu.
Musa
Ɗanba’u
Gidan Buwai yana amfani ne da kalangu wajen kiɗinsa, da kalangun ne ya yi wannan waƙar
noman da sauran waƙoƙinsa. Ita ma ya yi ta ne domin ya yi kira ga mutane da su
dawo da hankalinsu wajen noma. Ya rasu a lokacin da yake da shekaru 58 a ranar
Talata 07/04/2015. A sakamakon wata gajeruwar rashin lafiya. Ga mashahuriyar waƙar
tasa:
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.