Ticker

6/recent/ticker-posts

Naɗewa - Daga littafin “Bara Da Wasu Waƙoƙin Bara A Ƙasar Hausa

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

 Naɗewa

A wannan babin an kawo jigogin waƙoƙin da mabarata ke amfani da su wajen bara har ma tare da bayanai da misalai daidai gwargwado. An yi nazarin ƙumshiyar jigogin domin fito da yadda suke iya tasiri ga waɗanda ake yi wa bara ya sa su bayar da sadaka ba a cikin damuwa ba. Jigogin sun haɗa da na Wa’azi da na Madahu wato yabo da na Ilmantarwa da Nishaɗantarwa da Barkwanci da na Bantausayi da kuma na Fatan alheri. Duka duka, an sami jigogi takwas waɗanda wannan nazarin ya gano da suke ƙumshe a cikin waƙoƙin na bara. Dukan misalan da aka bayar daga waƙoƙin bara na baka ne domin su ne waƙoƙin bara na asali. Su rubutattu asalinsu ba na bara ba ne, mabarata ne kawai suka mayar da su na bara kamar dai yadda aka sha nanata faɗi a cikin aikin. Duk da haka an kawo wasu ‘yan misalai ƙalilan daga rubutattun waƙoƙin da ake bara da su saboda kawai mabarata na bara da su. Ba a waƙa ba tare da salo ba, domin ita kanta salo ce. Babi na gaba ne ya dubi salon waƙoƙin.


Post a Comment

0 Comments