Ticker

6/recent/ticker-posts

Nabiba

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Nabiba

 

G/Waƙa: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

 

Jagora: Ga mu dai muna yawatawa.

‘Y/ Amshi: Can wata rana ka iske mun kai ƙiyama,

: Daga jiya babu wane yau babu wane.

: Mutun kai kau zanka yi kana lissahwawa,

: Ka san komi tad daɗe tana kai gareka.

: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

 

Jagora: Duniya magajinki Allah.

‘Y/ Amshi: Al’amarin duniya wuya ag gare shi.

Jagora: Ba ni koma zuwa Gwaranyo roƙon abinci,

: Sai in dai Talatuwa ta kirai ni.

: Talatuwa..

‘Y/ Amshi: ‘Yam maigoro na yaba mat da hairan.

: Alhaji ko ba kiɗi  ina son Nabiba,

: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

 

 Jagora: Ni dai ko ban gida ina son Nabiba.

‘Y/ Amshi: Alhaji ko ba kiɗi ina son Nabiba,

: Ko yaran Ɗan’anace na son Nabiba.

 

Jagora: In dai kun san Nabiba na san Nabiba.

‘Y/ Amshi: Alhaji mun san Nabiba kyauta gare shi,x2

: In kai ya ba ka mai kiɗI mu ya bamu,

: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

 

 Jagora: .Duniya magajinki Allah,

‘Y/ Amshi: Al’amarin duniya wuya ag gare shi,

: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

 

  Jagora: A bar maka noma na Bawa manzon ciyawa.

: Mai sunah hatci.

‘Y/ Amshi: Giyen Ɗan’anace,

: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

 

 Jagora: A bar maka noma na Bawa manzon ciyawa.

: Mai sunah hatci.

‘Y/ Amshi: Giyen Ɗan’anace,

: Ya yi halin maza,

: Yana inda aiki.

Post a Comment

0 Comments