Ticker

6/recent/ticker-posts

Bajinin Danjimma Na Mani

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Bajinin Ɗanjimma Na Mani.

 

 G/Waƙa: Ya ɗau gaba da magarya,

: Bajinin Ɗanjimma na Mani.

 

 Jagora: Ga mai gona na kallo.

‘Y/ Amshi: Ga mai gona na kallo.

 

Jagora: Ga mai gona na kallo.

‘Y/ Amshi: Ga mai gona na kallo,

: Ya ɗau gaba da magarya,

: Bajinin Ɗanjimma na Mani.

 

Jagora: Gani inai maka horo Sani,

: Kai dai garje ka yi noma.

 ‘Y/ Amshi: Ko wac ce ya saki noma,

: Rani na watce gida nai,

: In ya korai ya yi ƙaura,

: Ya ɗau gaba da magarya,

: Bajinin Ɗanjimma na Mani.

 

 Jagora: To gani inai maka horo Sani,

: Don Allah dai ka yi noma.

‘Y/ Amshi: Ko wacce ya saki noma,

: Rani na hwaɗa gida nai,

: In ya korai yaji haushi.

 

 Jagora: Gasa.

‘Y/ Amshi: Ya ɗau gaba da magarya,

: Bajinin Ɗanjimma na Mani.

 

Jagora: To alheri kun ka yi Sani.

‘Y/ Amshi: Ba rowa kun ka yi man ba.

 

Jagora: To alheri kun ka yi Sani.

‘Y/ Amshi: Ba rowa kun ka yi man ba.

 

Jagora: Kowa hana mani samun duniya.

‘Y/ Amshi: Sai nai gaba da uwa tai,

: In ya ɓatan naji haushi.

 

Jagora: Kun san in dai magana ta kiɗi ce,

: Sai na zo in yi bayani.

: In yaro ya biɗi suna.

‘Y/ Amshi: In kau bai sami kiɗina ba,

: Ya zan buzu ga banawa[1],

: Ga ango babu amarya,

: Ya ɗau gaba da magarya,

: Bajinin Ɗanjimma na Mani.

 

Jagora: Kun san in dai magana ta kiɗi ce,

: Sai na zo in yi bayani,

: In yaro ya biɗi suna.

‘Y/ Amshi: In kau bai sami kiɗina ba,

: Ya zan buzu ga banawa,

: Ga ango babu amarya,

: Ya ɗau gaba da magarya,

: Bajinin Ɗanjimma na Mani.

 

Jagora: Ga mai gona na kallo.

‘Y/ Amshi: Ga mai gona na kallo.[1]  Matasa/samari.

Post a Comment

0 Comments