Ticker

6/recent/ticker-posts

Ɗanmalka Sani

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ɗanmalka Sani

G/Waƙa: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

 

 Jagora: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

‘Y/ Amshi: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

 

Jagora: Yana rabkak ƙasa,

: Tana watcewa da wargaji[1].

‘Y/ Amshi: Ya yi zuhwa kamab,

: Baya jin ciwon jikinai.

 

Jagora: Yana gabtaƙ ƙasa,

: Tana watcewa da wargaji.

  ‘Y/ Amshi: Ya yi zuhwa kamab,

: Baya jin ciwon jikinai.

 

  Jagora: Ƙanena ne.

 ‘Y/ Amshi: Ban ce ƙanen wani naba ko can.

 

Jagora: Kullun murna nikai.

‘Y/ Amshi: Ɗan’uwana zaya aure.

 

Jagora: Kanen Ɗancana gwarzon Sa’idu na Alhaji.

  ‘Y/ Amshi: Kuma na sarkin Barno Sani.

 

  Jagora: Han nai kamun ƙahwa.

 ‘Y/ Amshi: Inda Ɗanmanya da Dando,

: Da sarkin Barno,

: Nai gargarad doki a sai man,

: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

 

Jagora: In Allah ya yi baibaya..

  ‘Y/ Amshi: A yi ta ruwa da iska.

 

Jagora: In Haliƙu yay yi baibaya[2].

‘Y/ Amshi: A yi ta ruwa da iska.

: To in don kaba Bawa ce hadari ya taso.

 

 Jagora: Kowac ce baya son ka,

: Kai ma ce baka so nai.

‘Y/ Amshi: In ya tara samu ,

: Kamad dutcin Bakura.

: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

 

Jagora: Kowac ce baya son ka,

: Hak kai ce baka so nai.

‘Y/ Amshi: In ya tara samu,

: Kamad dutcin Bakura.

 

Jagora: Yaro na yi ma yawa.

‘Y/ Amshi: Ko can baka isan ba.

 

Jagora: Yaro na yi maka yawa.

‘Y/ Amshi: Ko can baka isan ba.

 

Jagora: In kin hi Magajiya,

: Wadda tas saba da nema.

‘Y/ Amshi: Tunjere da ɗai,

: Bawa ya hi gaton budurwa,

: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

 

  Jagora: Abokan maganammu,

: Sai an wuce gora da Rini.

‘Y/ Amshi: Sai an wuce Gora da Rini,

: Bale Janbaƙo,

: Ko Hwaru sun ji irin ɗumina,

: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.

 

  Jagora: Shina labtaƙ ƙasa,

: Tana watcewa ga kuyye.

‘Y/ Amshi: Ya yi zuhwa kamab,

: Baya jin ciwon jikinai.

: Bai zanna ba gona,

: Gaba Ɗanmalka Sani.[1]  Wani babban abin bugu kamar salleta/masaba.

[2]  Rufin asiri.

Post a Comment

0 Comments