Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Wanke Wa Yarona Bahaya, Ya Matsayin Alwalata?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam ni ce na yi alwala sai yarona ya yi bahaya, sai na wanke masa. Shin zan sake yin wata alwala ce koko zan iya sallah da ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu. Ƴar uwa alwalarki tana nan, kuma za ki iya yin sallah da ita, abin da kawai za ki yi shi ne, bayan kin gama wanke wa yaron bahayar, sai ke ma ki sa hannunki a ƙasa ki wanke tare da ƙasar, ko kuma ki sa sabulu ko omo, ko wani sinadarin makamantansu. Saboda ai ba ke ce kika yi bahayar ba, kuma dama malaman Fiƙhu sun kasa tsarki zuwa gida biyu ne, wato tsarkin hadasi da tsarkin khabasi, kuma dukkansu ibada ba ta inganta sai da su, kuma su ma ba sa inganta sai da ruwa mai tsarki kuma mai tsarkakewa.

1. TSARKIN HADASI (طهارة الحدث): Abin da ake nufi da tsarkin hadasi shi ne tsarkake najasar da ke fita ta hanyoyin nan guda biyu, wato dubura da gaba (zakari ko farji), kamar fitsari da maziyyi da bahaya da sauransu.

2. TSARKIN KHABASI (طهارة الخبث): Wannan kuma nau'i ne na tsarki da ya shafi tsarkake wurin sallah, da tufafin mai sallah, da darduma ko tabarma ko najasar da ta taɓi jikin mai sallah, da makamantan haka.

Wannan nau'in tsarki na biyun shi ne hukuncin wanda ta wanke wa yaronta bahaya bayan ta yi alwala, wato alwalarta tana nan, wanke hannun kawai za ta yi.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IƙsWWSpUkwk6b8hWJ6vXOO

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments