Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Yunkura Raka’a Ta Biyar A Sallah, Ya Zan Gyara?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam. Tambyata ita ce, a cikin sallah ce mutum zai yi raka'a 4, wajen zama tahiya sai ya manta ya tashi, ya zai yi ya gyara malam?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam. Idan mutum ya kammala adadin raka'o'in sallarsa, a maimakon ya zauna ya yi tahiya ya yi sallama, sai ya mance ya miƙe zai ƙara kawo wata raka'a ta uku a sallah mai raka'a biyu, ko ta huɗu a sallar Magriba, ko ta biyar a sallah mai raka'a huɗu, to hukuncinsa shi ne, idan har ya tuna kafin ya ƙulla ruku'u a wannan raka'ar da yake kan ƙarawa, to zai dawo ya zauna ne ya yi tahiya, ya yi sallama, sannan bayan ya idar da sallar sai ya yi sujjada ba'adiyya.

Idan kuma ya riga ya ƙulla ruku'u sannan ya tuna, to ba zai dawo ba, zai ci gaba da yin wannan raka'ar ce kawai, idan ya kai ƙarshenta sai ya zauna ya yi tahiya, ya yi sallama, sannan kuma sai ya yi sujjada ba'adiyya.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments