Matsayin Shiga Bayi Da Waya Mai Alƙur’ani

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Malam ni ce wata tana da compiled Ƙur'an shin zan iya shiga bayi da ita domin haska fitilar wayata?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Game da shiga bayi da waya (handset) mai ƙunshe da Alƙur'ani a ciki, malaman Musulunci sun bayar da fatawowi a kai, musamman ma na zamanin da muke ciki, wanda a ciki ne aka sami wayar salula mai ɗauke da Alƙur'ani.

    Kai tsaye dai shiga bayi da Alƙur'ani haramun ne sai idan akwai lalura mai girma. Hadisin da Anas Allah ya ƙara masa yarda ya ruwaito, wanda yake cewa "Annabi idan zai shiga bayi yana cire zobensa" ya yi nuni a kan haka, domin an ce rubutun da ke kan zoben shi ne "MUHAMMADUR RASULILLAH" (محمد الرسول الله), wanda kuma wannan wani ɓangare ne na wata aya a Alƙur'ani. Abu Dawud 19, Tirmizhi 1746, Nasa'i 178, Ibn Majah 303.

    Amma kuma idan mutum yana jin tsoron in ya ajiye Alƙur'aninsa a waje ya shiga bayi za a iya sace masa, wasu malaman sun ce ba laifi idan ya shiga da shi bisa wannan lalurar, kamar yadda Sheikh Ibn Baz ya bayyana a Majmu'u Fatawa. Duba Majmu'u Fataawa na Ibn Baz (10/30).

    Amma kuma idan Alƙur'anin yana cikin salula ne ba laifi idan an shiga da salula ɗin, sai dai an karhanta (ƙyamaci) a buɗe Alƙur'anin wayar salular a cikin bayi, ko kuma idan ya kasance akwai rubutun Alƙur'ani a jikin screen ɗin wayar, shi ma wannan an karhanta shiga da shi bayi, domin shi ma kamar wanda ke kan zoben can ne, wato kenan idan a cikin wayar ba buɗe Alƙur'anin aka yi ba babu laifi.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.