Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Mande Labbo Ankara

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Na Mande Labbo Ankara

  G/Waƙa: Da aniya yaka  noma,

: Na Mande Labbo Ankara ka sha rana.

  Jagora: Yau da gobe sai mai ƙarhi.

  ‘Y/ Amshi: Yaro a zan gwada mashi ‘yan kuyye nai.

 

  Jagora: Yau da gobe sai mai ƙarhi.

  ‘Y/ Amshi: Yaro a zan gwada mashi ‘yan kuyye nai.

: Da aniya yaka noma,

: Na  Mande Labbo Ankara ka sha rana.

 

  Jagora: Mamman Dan Labbo ya mani doki.

  ‘Y/ Amshi: Mamman Dan Labbo ya mani doki,

: Ya kara ma da diyan makiyana haushi,

: Da aniya yaka  noma,

: Na Mande Labbo Ankara ka sha rana.

 

  Jagora: Kasan ba’a dariyar mai noma.

  ‘Y/ Amshi: Ko baya ci ya maida abinai kuɗɗi,

: Da aniya yaka  noma,

: Na Mande Labbo Ankara ka sha rana.

 

  Jagora: Kasan ba’a dariyar mai noma.

  ‘Y/ Amshi: Ko baya ci ya maida abinai kuɗɗi,

: Da aniya yaka  noma,

: Na Mande Labbo Ankara ka sha rana.

 

  Jagora: Duk wanda ya aje kuɗɗi.

  ‘Y/ Amshi: Nai tammahar ya ‘yammani ‘yan kuɗɗinai.

 

  Jagora: Duk wanda ya aje kuɗɗi.

  ‘Y/ Amshi: Nai tammahar ya ‘yammani shi in yaso.

 

  Jagora: Faɗa ma wanda yaz zo.

  ‘Y/ Amshi: To nasa tammahar ya ‘yammani ɗanyen kihi,

: Da aniya yaka  noma,

: Na Mande Labbo Ankara ka sha rana.

 

  Jagora: Ɗiya maza jiki kuka so.

  ‘Y/ Amshi: Kun lwaye gida kunai mana kurin banza.

 

  Jagora: Kamar garin da babu maza.

  ‘Y/ Amshi: Kun sa gazama ta nai mana ko-ta-kwana[1],

: Da aniya yaka  noma,

: Na Mande Labbo Ankara ka sha rana.



[1]  Shirin Fuskantar wani abu a kowane lokaci.

Post a Comment

0 Comments