Ticker

6/recent/ticker-posts

Maidamma Giyen Mani

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Maidamma Giyen Mani

 

 G/Waƙa: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Ƙaro gaba mai ƙarhi.

  ‘Y/ Amshi: Giye ƙaro gaba mai kai gayya.

 

  Jagora: Ƙaro gaba mai ƙarhi.

  ‘Y/ Amshi: Giye ƙaro gaba mai kai gayya.

 

  Jagora: Na gode Allah Makau.

  ‘Y/ Amshi: Na gode mutan shiyyag ga,

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Dawaki ya sawo mani doki,

: Ya  ba ni biya na amsa.

  ‘Y/ Amshi: Ko da yab biya dokin,

: Ban ko mai da kiɗan dokin ba,

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Dawaki ya sawo mani doki,

: Ya  ba ni biya na amsa.

  ‘Y/ Amshi: Ko da yab biya dokin,

: Ban ko maida kiɗan dokin ba.

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Rad da Giwa yai mani dokin,

: Naɗ ɗora gwadi nai rannan,

: Waɗansu sana murnata,

: Su wane ana gintcewa[1],

: Kai garinmu ana durin uwa.

 ‘Y/ Amshi: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

.

  Jagora: Giwa kana daga da haki.

  ‘Y/ Amshi: Giwa kana daga da haki,

: Kan-kan-kan,

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Ƙaro gaba mai ƙarhi.

  ‘Y/ Amshi: Giye ƙaro gaba mai kai gayya.

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Giye wanda yay yi nisa.

  ‘Y/ Amshi: Shi aka kwana kira,

: Yana ƙyalewa.

 

  Jagora: Giye wanda ya yi nisa.

  ‘Y/ Amshi: Shi aka kwana kira,

: Yana ƙyalewa,

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

  Jagora: Giye sai tsakar dare yaka noma nai,

: In babu mutane hwalke,

: To da shi da mutanen ɓoye.

  ‘Y/ Amshi: Duw wanda yah hwalka,

: Yaz zo raɓa ta hwashe mai ƙwabri.

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Giye sai tsakad dare yaka nomanai,

: In babu mutane hwalke[2],

: To da shi da mutanen ɓoye.

  ‘Y/ Amshi: Wanda yah  hwalka,

: Yaz zo raɓa ta hwashe mai ƙwabri.

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Giwa kana daga da haki.

  ‘Y/ Amshi: Giwa kana daga da haki.

: Kan-kan-kan.

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Ya yi shiri yankam ma bugaje.

  ‘Y/ Amshi: Ya yi shiri yankam ma bugaje ƙamna,

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.

 

  Jagora: Na gode Allah Makau.x2

  ‘Y/ Amshi: Na gode mutan shiyyag ga.x2

: Maidamma giyen Mani,

: Ba rana yaka ji daji ba.



[1]  Game fuska/ɓata rai.

[2]  Farke wato ba bacci suke yi ba.

Post a Comment

0 Comments