Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Lawali

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Na Lawali

 

  G/Waƙa: Kai dai na Lawali riƙe aiki da gaske,

 

 Jagora: Kai dai gwamatsa ma noma

: Tushen Hashimu.

 ‘Y/ Amshi: Na hi son kana kwana bakin dawa[1],

: Na tahho gani nai gojen Hashimu,

: Ya kashe balasar  daji Ɗahiru.

 

 Jagora : Kai dai gwamatsa ma noma

: Tushen Hashimu,

 ‘Y/ Amshi: Duk wanda baya ƙwazo[2],

: Ɓaci nai mukai.

 

 Jagora: Duk ɗan da baya ƙwazo.

 ‘Y/ Amshi: Ɓaci nai mukai,

: Na taho gani gojen Hashimu,

: Ya kashe balasad daji Ɗahiru,

 

  Jagora: Ku yi noma ku tadda masu,

: Daraja a duniya.

 ‘Y/ Amshi: Kowa aje dami ya zauna lahiya,

: Na taho gani nai gojen Hashimu,

: Ya kashe balasad[3],

: Daji Ɗahiru.

 

 Jagora: Tahiyar da na yi don Ɗan labbo nay yi ta.

 ‘Y/ Amshi: Abinda na faɗamai badawa yakai.



[1]  Gona ken an wajen aikin noma.

[2]  Noma

[3]  Wani hakin daji ne wanda manoma bas u so a gonarsu, yana da kauri kuma idan ka murza ruwansa yana da yauƙi sosai.

Post a Comment

0 Comments