Ticker

6/recent/ticker-posts

Iyalin Dan jumma

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Iyalin Ɗan jumma

 

 G/Waƙa: Ya riƙa gona da anniya,

: Ga Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.

 

 Jagora: Hirgita gona ƙanen magaji.

 ‘Y/ Amshi: A bar maka noma ka yi ta yi,

: Ya riƙa gona da anniya,

: Ga Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.

 

 Jagora: Ɗanlamso Ɗan Tashikka Ɗan Shawai.

 ‘Y/ Amshi: Ɗan Tashuka Ɗan Shawai.

: Biɗi kwashe[1] ka yi zahwa[2],

: Ya riƙa gona da anniya,

: Ga Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.

 

 Jagora: Ga iyalin Ɗan jumma nit taho,

 ‘Y/ Amshi: Sun san riƙa turu da ƙa’ida.

 

 Jagora: In hairan na yi duniya.

 ‘Y/ Amshi: Duk tare da Ɗan jumma niy yi shi.

 

 Jagora: Kuma in sheri niy yi duniya.

 ‘Y/ Amshi: Dut tare da Ɗan jumma niy yi shi.

 

 Jagora: Lalle in sheri niy yi duniya.

  ‘Y/ Amshi: Dut tare da Ɗan jumma niy yi shi.

: Ya riƙa gona da anniya[3],

: Ga Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.

 

 Jagora: To na yi saduda da hamdala,x2

 ‘Y/ Amshi: Hasken ‘yan gayya da ya wuce,

: Allahu ya gammai[4] da gafara,

: Ya riƙa gona da anniya,

: Ga Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.x2

 

 Jagora: Ɗan lamso ɗan Tashuka Ɗan Shawai.

 ‘Y/ Amshi:: Biɗi kwashe ka yi zahwa[5].

 

 Jagora: Kowa yazo kasuwa ranar juma’a,

 ‘Y/ Amshi: Ya san zahwa ta gyra duniya.

 

 Jagora: Da akwai rogo naga dankali.

 ‘Y/ Amshi: Hat tare da janjare[6] zay yawa,

: Ya riƙa noma da anniya,

: Ga Hashimu Ɗan Labbo niz zaka.

 

  Jagora: Ga iyalin Ɗan Jimma nit tahho.

  ‘Y/ Amshi: Sun riƙa turu da ƙa’ida[7].



[1]  Magirbi

[2]  Kaftu.

[3]  Da gaske wato suna yin aikin gona kamar yadda ya kamata.

[4]  Sadar da shi/ yi masa.

[5]  Kaftu, 

[6]  Jar dawa.

[7]  Suna biyan waƙa daidai.

Post a Comment

0 Comments