Dan Bawa

     Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    ÆŠan  Bawa

     

     G/WaÆ™a: Ya tara dami mai dama,

    : ÆŠan  Bawa ÆŠanen mai gona.

     

     Jagora: Dubun ÆŠan  Bawa,

     ‘Y/ Amshi: Na manuga jikan bana.

    : Kai munka sani tun farko,

    : Ya tara dami mai dama,

    : ÆŠan  Bawa ÆŠanen mai gona.

    Jagora: Dubun ÆŠan  Bawa,

     ‘Y/ Amshi: Nufin Allah ne,

    : Allah ya yai mai huÉ—uba mai tasai,

    : Ya tara dami mai dama,

    : ÆŠan  Bawa Æ™anen mai gona.

     

     Jagora: ÆŠan  Bawa inai ma horo.

     ‘Y/ Amshi: Kai dai ka tsare horo na.

     

      Jagora: Horon da nikai maka.

      ‘Y/ Amshi: Arna kowa ya riÆ™e mata tai.

     

     Jagora: Kowa ya yi dubu har ya yi rabo.

     ‘Y/ Amshi: Ya É—au[1] maganar kaka nai,

    : Ya tara dami mai dama,

    : ÆŠan  Bawa Æ™anen mai gona.

     

     Jagora: Dogo ÆŠan  Bawa.

     ‘Y/ Amshi: HwaÉ—in[2] Allah ne.

     

    Jagora: Kullun na zaka wurin yawona,

    : Ina iske mijin ‘Yas suntau.

    ‘Y/ Amshi: Sai ya  ba ni dami in É—auko,

    : Ya tara dami mai dama,

    : ÆŠan  Bawa Æ™anen mai gona.

     

     Jagora: Mai kasuwa.

     ‘Y/ Amshi: Ban dai rena ba,

    : Riga ta ƙwarai ya sa min,

    : Domin ka ƙanen mai gona.

     

     Jagora: Sarkin noma Æ™anin ‘yar burmau,

     ‘Y/ Amshi: Ban dai raina riga ta Æ™warai ya samin dami,

    : Domin ka ƙanin mai gona.

     

     Jagora: ÆŠan Mairi.

     ‘Y/ Amshi: Ban dai raina riga ta Æ™warai ya samin dami,

    : Domin ka ƙanin mai gona.

    : Ya tara dami mai dama,

    : ÆŠan  Bawa Æ™anen mai gona.



    [1]  Yin amfani da abin da aka hore shi.

    [2]  FaÉ—ar Allah, abin da Allah ya nufa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.