Na Ga Batsar Da Mijina Yake Rubuta Wa Wata A Waje

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum, Malam, ni ce na ga batsar da mijina yake rubuta wa wata a waje. Zan iya fuskantar shi da zancen ko kuwa? Ina neman shawara, na kasa sakewa, malam.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

    A asali wajibi ne a kan dukkan musulmin da ya ga wani abin da ba daidai ba ya gyara shi, ya mayar da shi daidai da gwargwadon ikonsa da iyawarsa, kamar yadda ya zo a cikin Hadisi. Amma dai dole hakan ya zama da hikima da kyakkyawan wa’azi, kamar yadda aya ta nuna. Shari'a ta haramta yasashshen zance a aya ta 3 a Suratul Muminun:

    وَالَّذِينَ هُمْ عَنِ اللَّغْوِ مُعْرِضُونَ

    Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne.

    Zancen Batsa ta hanyar Ƙiran Waya ko rubutaccen saƙo, wannan wata Musibace da Fitina wacce ta addabi Al'ummar wannan Zamani damuke cikinsa, tun daga kan Maza har Mata, masu aure da marasa aure, kuma wajibine akan masu wannan aiki suyi gaggawar tuba zuwa ga Allah.

    Azaba mai radadi da wulakantarwa ta tabbata bisa waɗanda suke hirar batsa indai har basu tuba. Kuma yana daga cikin hanyar da zata kai zuwa aikata zina. Allãh Yana cewa:

    وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَسَآءَ سَبِيل

    Kuma kar ku kusanci zina, lallai ne shi alfasha ne kuma mummunar hanya ce.

    Yana daga cikin manyan ka'idojin sharia toshe hanyar da take kaiwa zuwa ɓarna.

    Don haka, wannan matar da ta ga abin da mijinta yake yi mara kyau, wajibi ne ta ɗauki matakin gyara shi, ta mayar da shi daidai. Don haka, sai ta fuskanci mijin da Magana a kan abin da ta ga ya yi ba daidai ba, amma da kyakkyawar manufar gyara shi. Kuma ya zama da hikima, ta yadda abin ba zai haifar da wata ɓarnar da ta fi wadda yake aikatawa ba.

    A nan kuma lallai ma’aurata su yi taka-tsantsan game da binciken wayoyin junansu, domin ta nan ne ake ganin irin abubuwan da suke haifar da irin wannan. Allaah ya kiyaye.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.