Hukuncin Wanda Yayi Rantsuwa Ba Zai Sake Aikata Saɓo Ba, Sai Kuma Ya Sake Aikata

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene Hukuncin Wanda Yayi Bakancen Bazai Sake Aikata Wani Saɓo Ba Dayake Aikatawa, Saikuma Ya Aikata Saɓon Shin Zayi Kaffarane?

    ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Shi bakance asalinsa makaruhine bai kamata mutum yayi bakance akan wani aikin alkhairi ko saɓo ba, Saboda faɗin Annabi ( Bakance baya zuwa da alkhairi, kuma yana fitowa daka marowacine) Nisa'i ( 3801) Albani ya ingantashi acikin Sunan Nisa'i.

    Shaik Usaimeen rahimahullah ya ce: Muna yiwa 'yan'uwanmu nasiha akan kada mutum yayi bakance akan dena saɓo, dan kada hakan yazamo masa al'ada, tayanda baya iya barin aikin saɓo sai inyayi bakance, Allah maɗaukakin sarki ya ce:

    وَأَقْسَمُوا بِاللَّهِ جَهْدَ أَيْمَانِهِمْ لَئِنْ أَمَرْتَهُمْ لَيَخْرُجُنَّ ۖ قُلْ لَا تُقْسِمُوا ۖ طَاعَةٌ مَعْرُوفَةٌ ۚ إِنَّ اللَّهَ خَبِيرٌ بِمَا تَعْمَلُونَ

    Munafukai suna rantsuwa da Allah iyakar rantsuwa idan Annabi yai musu izinin fita jihadi, zasu fita, Allah ya ce: Kace dasu kada su rantse akan karya, biyayyarku sananniyace da harshece kawai.

    Kamar hakane ba a bukatar yin bakance akan daina saɓo ko aikin alkhairi, abunda akeso shi ne ka ƙulla niyyar mai karfi ta dena saɓon ko jajircewa wajan aikin alkhairi batare dayin bakanceba, wannan shi ne abunda yafi alkhairi.

    Wanda yayi bakance akan bazai kara aikata wani saɓo ba sai kuma ya aikata, wajibine yatuba yayi istigfari saboda aikata wannan saɓon, dakuma rashin cika wannan bakancen, sannan yayi kaffarar rantsuwa, shi ne ciyar da miskinai goma, ko tufatar dasu, ko 'yanta baiwa, waɗannan abubuwan guda uku cikinsu zai zaɓi ɗaya yayi, mutum zaiyi wanda yakeso acikinsu, idan bai samu damaba sai kayi azumi guda uku.

    Dan haka dolene sai kayi kaffarar rantsuwa, sannan kuma saikayi istigfari da tuba akan aikata wannan saɓon.

    WALLAHU A'ALAM

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.