Ayar Da Ke Magana A Kan Kisfewar Wata

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum malam  an wuni lafiya ina da tambaya, ina son a fadamin ayar da yake magana akan kisfewar wata.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus salamu. Ban fahimci wace aya ce kike nufi a kan kisfewar wata ba, in kuma waɗannan ayoyin na suratul Ƙiyama ce kike nufi, to kuma ban fahimci me kike so a fitar a game da su ba, amma dai ga su nan acikin suratul-Ƙiyama Ãya ta 7 zuwa 13:

    فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ

    To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).

    وَخَسَفَ الْقَمَرُ

    Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).

    وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ

    Aka tãra rãnã da watã

    يَقُولُ الْإِنْسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ

    Mutum zai ce a rãnan "Ina wurin gudu?"

    كَلَّا لَا وَزَرَ

    A´aha! bãbu mafaka.

    إِلَىٰ رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ

    zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.

    يُنَبَّأُ الْإِنْسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ

    Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.

    Kuma na dai san cewa a hadisai ingantattu Annabi ya ce:

    إن الشمس والقمر آيتان من آيات الله، لا ينكسفان لموت أحد ولا لحياته، فإذا رأيتم فصلوا وادعوا الله.

    MA'ANA:

    Lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah, ba sa kisfewa saboda mutuwar wani mutum ko rayuwarsa.

    A ƙarshen hadisin sai Annabi Ya ce: Duk lokacin da kuka ga hakan, to ku tashi ku yi sallah, ku yi ta addu'a har a yaye maku (kisfewar).

    A duba Sahihul Bukhari, babin da ke magana a kan sallar kisfewar rana, hadisi mai lamba ta 996. Wannan shi ne abin da ya tabbata daga Annabi

    Allah ne mafi sani.

    JAMILU IBRAHIM SARKI, ZARIA.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/EbkKRXdFzNu4F8aƘZbZ1Vx

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.