Ticker

6/recent/ticker-posts

Muhammadu Mai Noma Da Mutanen Boye

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Muhammadu Mai Noma Da Mutanen Ɓoye

 

G/ Waƙa: Ai Muhammadu ɗan Mamman na,

: Mai noma da mutanen ɓoye.

 

Jagora  : Dodo ba a zame ma Dodo Mamman,

: Ko kai ka isa Dodon kanka,

: Ai ku tattaro kui kallo,

: Maza ku tattaro ku yi kallon hurde,

: Ai ga hurde ga hannun Hauwa Mamman.

: Ai ɗan ‘Yallabbo manomin gaske,

: Mai noma da mutanen ɓoye,

: Jikan Kande manomin gaske,

: Dodo ba a zame ma Dodo,

: Ai ba mamaki manomin gaske Mamman.x2

 

 Jagora : Ku tattaro kui kallo,

: Ai tunda abin magana ya samu,

: Yau sharabonmu da kyautad doki?

: Ai dokin hwaihwai aka yayi Mamman,

: Dokin hwaihwai aka yayi yanzu Mamman,

: Mamman ya biya ya kyauta man,

: Yau ga hurde[1] ga hannun Hauwa,

: Ai ga hurde ga hannun Hauwa Mamman.

 

 Jagora: Tun assalati na kukan kaza,

: Tun kukan zakaran hwarawa,

: Ya jawo wani babban walki,

: Ya ɗauko wani babban gora,

: Ya ɗauko haɓaton kalmen nan,

: Shi mai ce ma haki tai hwaɗi,

: Tai hwaɗi a sare gindi,

: A ba rana ajiya hag gobe.

 

  Jagora : Jikan Kande manomin gaske Mamman,

: Kande in da dawo[2] maza dama,

: Ke dama tsaye ɗebe luddai,

:Ya ga naway ya tsaya kamawa,

: In kuma babu dawo shi kenan,

: Mamman ya tahi bai hwasawa,

: Sha bauri yita yin aikinka,

: Don noma da dawo sai yara,

: Ai muhammadu sha bauri yita yin aikinka,

: Don noma da dawo sai yara Mamman.

 

 Jagora : Ai Dawa Tsoho ya kyauta,

: Ai ka ga Dawa tsoho ya kyauta,

: Ƙarangiya ma ya kyauta min Mamman,

: Ai ‘Yallabo ta biya ta kyauta min  Mamman,

: Ai ga waren masaki nan Mamman,

: Kigo babu abin burkewa,

: Ai ga wata ‘yam Magana ta samu,

: Ai ku nura da mai kuri da

: Gidan gadonsu Mamman,

: Shi bai cimma gidan gadon ba,

: Sannan ya ƙi duhu don tsoro,

: Da gaban na shiga ban ɗauka ba,

: Ƙwamma ciro ka ci ba sata ba,

: Ko an gane ka ana ƙyale ka,

: Amman a shiga ban ɗauka ba,

: Wannan bata raba ka da gaba,

: Ai ga ɗa guda da kamaɗ ɗa metin Mamman.



[1]  Sunan doki ne, mai ɗoshin lafiya.

[2]  Fura.

Post a Comment

0 Comments