Ticker

6/recent/ticker-posts

Dawai Jikan Magaji

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Dawai Jikan Magaji

 

 G/ Waƙa: Tataushe  gamba dawai,

: Mai zwarin daji,

: Jikan magaji bai raga noma ba,

: Ai in dai halin mijina ya tashi,

: Bai san dareba,

: Ko da wane lokaci,

: Ya ta da batun aiki,

: Zakin Balarabe mai gangumma,

: Dogo baban Bala,

: Doki kalangunka dogo,

: Ɗan malam uban kiɗi,

: Kuma ya kyauta,

: Mijin Ladi ya biya ni,

: Ya biya na gode,

: Ai Abubakari na iske,

: Ka biya ka kyauta,

: Bawa ya biya kan na gode,

: Ta Baraka Allah  ya ba ku,

: Gobe kuna  ba ni.

 

 Jagora :To ku riƙa da gaskiya domin Allah,

: Da kai nike jikan magaji mai rana mugu,

: Dawaiyye dokin noma,

: Ai warinka[1] ba su koma batun aiki,

: Ko gardama da kai sai ka barsu,

: Buzu ma  shakurum baɗi ya ɓaci,

: Na yar rikici kai madun kurum warin daji,

: Zaki magarya bai ra noma ba,

: Mijin Hajo bai san dare ba,

: Bai san dare ba,

: Ai magaji da ranakka,

: Allah ya taimakai ya cece ni.

 

 Jagora: Ai ni Kulu,

: Ni kulu Hwati[2] tai kira na amsa,

: Ai ni Kulu Hwati tai kira na,

: Na gode Hwati ‘yar manya mutane,

: Ta Mairin Amadu ki garaje,

: Hwati tai komi mutane,

: Kun ga tuhwahi[3] nan na hwati,

: Ni kulu na gode ma hwati,

: Ai kulu hwati tai kirana,

: Ɗiyah Hajiya maimuna sannu hwati,

: Ɗiya Alhaji na Allah hwati na yaba ta,

: Ni kulu hwati tai kirana.

 

Jagora: Ai to kuma na amso kiranta,

: Tunda sabtu isa amsa isa,

: Amma ga Ɗan kirki mutane,

: Amma ba Ɗan ƙo dogo ba,

: Mai amsar sabtu machuci,

: Abada bai tcerema zargi,

: Ko wacce ma,

: Haƙiƙa amsa ba musunai,

: Abin nan ko da ya yi tcada,

: Baya faɗi in ga idon ka,

: In dai ga kunyar mutane,

: Gidansu hwati aljannah maroƙa,

: Na sha daɗi in da huti,

: Hura ta gero ga nononta mankas[4],

: Ai tuwo na shinkahwa namanshi mankas,

: Ga ruwan firjin nan an aje min,

: Ga fanka nan ta motci.

 

Jagora: Gidansu Hwati aljannar maroƙa,

: A gaida sabon gero taushe suna,

: Hwati farin wata sa hasken duniya duk,

:Abinda kiy yi mani Hajiya na yaba ki,

: Ga tsokoki an zuba min,

: Ga ruwan firjin nan an ake min,

: Ga fanka nan na ta motsi,

: Gidansu Hwati aljannar maroƙa,

: A gaida sabon gero taushe sunah,

: Hwati farin wata sa haske duniya duk,

: A binda ki mani Hajiya na yaba ki,

: Allah taimake ki da hairan sannu Hwati,

: Hwati ta Mairin Amadu nayaba ta,

: Ni kulu na sha daɗi ga hwati,

: Ta  ba ni hwan ɗari,

: Ta yi min ɗunkin gayu mutane,

:An yi datcam mata ta miƙa min.



[1]  Waɗanda ake ‘yan shekara ɗaya, sa’o’in juna.

[2]  Suna ne na mata wato Fatima – Fati.

[3]  Tufafi/sutura.

[4]  Da yawa kenan ko wadatatacce.

Post a Comment

0 Comments