Ticker

6/recent/ticker-posts

Garba Na Yabo

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Garba Na Yabo

 

 G/ waƙa: Sa maza gudu mai raba gardama,

: Garba jan zaki.

 

  Jagora: To mu je gaba madalla Garba,

: Mai yi ma noma bugun tambarin yaro,

: Ina Garba na Yabo bai san da rana ba,

: Ai wassaka ni, wa maska ni,

: Ka zan tabbataw wada,

: Inda uwab Bala mai dubun mato,

: Ai inda uwak Kini mai dubun mato,

: Ai Garba,

: Ka dai gama da hanƙuri,

: Garba ka hanƙure mani.x2

: Abu Garba ka hanƙure mani,

: Garba na Yabo bai san da rana ba.

 

 Jagora: Garba Ɗanmaliki sai marece wurin aiki,

: Mai kwana yana lisahin aiki,

: Yabo akwai ɗiya maza,

: Yabo akwai mazaizan biɗad dawa,

: Ni kulu na san ɗiya mazan,

: Ni Kulu ko mazaizanmu sun san ni,

: Yabo kun taimaki Hauwa mai kodalin aiki,

: Ai Yabo kun taimaki Hauwa mai sa maza aiki.

 Jagora : Ai wassaka ni, wa maska ni,

: Ka zan tabbataw wada,

: Ɗebe batun kiɗi da ak kiɗe,

: Ko na bari mi ka sha man kai?

: Ni kulu na ji an yi liman,

: Wasu basu bi nai dadaɗin rai,

: To bare kiɗi kiɗe ko na bari,

: Mi ka sha man kai?

: Don dai galibin mutane,

: Halin mutane dun na shanu ne,

: In dai nagge ta ga ɓanna,

: Aniya takai don a koro ta,

: Ko an bat tata yi ɓanna,

: Ɓannag go ko ɓata ƙwasshe ta,

: Ɓannak kai takai don biɗam magana,

: Allah dai ya taimaka,

: Tabaraka Allah ya ba ‘Yanmaza sa’a.

: Abu da matansu ko sun ji daɗinsu,

: Na Sadiyya Garba bai san da rana ba,

: Na Mairi mai kai marece wurin aiki.

 

  Jagora : Ƙanen muhammadu Garba.x2

: Garba maƙi gudu maigidana ne,

: Ka ga su wane su ka gayyat taɓi,

: Da kaɗassu taɗ ɗwaɗe[1],

: Sai gayya yakai da kainai,

: Mata aniya kukai tunda ta ɗwaɗe,

: Sabko kukai tunda ta ɗwaɗe,

: Tun ba a jinjima ba mata,

: Sai ga itace ga kanunsu

: Sai wata tambaya yakai,

: Shanu sun yi ɓanna ga kaɗakka,

: Sun ce ja ka ban wuri,

: Kai hakanan kakan hwara ƙaryakka.

 

 Jagora: Kaɗakka[2] ko ƙuje bai hwaɗa ba,

: Sai in hwa bayanmu,

: Ai dai ƙwazo yana da daɗi,

: Kai ga irin wanda kas samu.

: Ya rangame na auna,

: Amsa yakai har a yo taɓi[3],

: Ya bar su sai ma’auni,

: Hwaɗin[4] ma’aunin kamaf fanka.

: Inda dai da zucciya,

: Da kowa ka ce sai ta ɗau tata.

: Sai ka yi sunanka tungurun,

: Ka huta da laihin biyab bashi.

: Ka ga su wane na ta kware ɗaki,

: Suna baibaye zaure.

: Halama kun hi son zaure,

: Kun hi cin moriyaz zaure?

 

  Jagora : Ai bakin yini sukai,

: Hauwa uwat Tuni bana kwana ba.

: Ka ga su wane na ta kware munta,

: Suna dwaɗe bayansu.

: Halan ruhwan ɗuwan ‘yan bori,

: Kukai don ku sha iska.

: Inji uwab Bala mai dubun mato,

: Garba Ɗanmaliki ka biyasheni na gode.

: Ai na Salihu mai kai marece wurin aiki.

: Mazana ku gama da hanƙuri,

: Allah ɗai yaz zan guda maza,

: Ai ya ishi duniya maigida Garba.[1]  Fashewa.

[2]  Audugarka.

[3]  Cirar auduga idan ta ƙosa.

[4]  Faɗi.

Post a Comment

0 Comments