Ticker

6/recent/ticker-posts

Muƙaddima - Daga Zababbun Wakokin Mawakan Baka Na Noma

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Muƙaddima 

Da sunan Allah mai Rahma mai Jinƙai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabin Rahama Muhammadu (SAW) da iyalan gidansa da sahabbansa da waɗanda suka yi koyi da su da kyautatawa ya zuwa ranar sakamako.

Marubucin Littafin Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Mawaƙan baka Na Noma Dr Haruna Umar Bunguɗu, ya yi tunani mai kyau ƙwarai da gaske, na ware waƙoƙin noma su kaɗai, ya fito da su, musamman idan muka dubi muhimmancin sana’ar noma ga Hausawa. Saboda haka, littafin zai yi amfani sosai ga ɗaliban gaba da Sakandare a fannin adabi.

Littafin Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Mawaƙan Noma, ya taskace waƙoƙin noma sama da ɗari (100) daga zaɓaɓɓun mawaƙan Hausa daban-daban. Sannan kuma, kowane mawaƙin aka taskato waƙoƙinsa, sai an kawo taƙaitaccen tarihin rayuwarsa, don sanin shi ko wane ne a fagen waƙa. Duk wani ɗalibi ko malami mai nazarin adabi, zai yi murna da haba-haba da wannan littafi, domin ya rage masa wahalar taskace waƙoƙi a wajen nazari.

Saboda haka, ina kira ga malamai da ɗaliban Hausa da sauran jama’a masu sha’awar nazarin adabi, su hanzarta su mallaki wannan littafin, da zarar ya samu fitowa. Fatana shi ne Allah Ya sanya albarka. Allah Ya yi mana jagora.

Yakubu Aliyu Gobir
SashenNazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Post a Comment

0 Comments