Ticker

6/recent/ticker-posts

Gabatarwa - Daga Zababbun Wakokin Mawakan Baka Na Noma

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Gabatarwa

Wannan littafi ya ƙunshi wasu zaɓaɓɓun waƙoƙin Hausa ne waɗanda mawaƙan baka suka yi na noma, wannan tunani na in yi wani aiki a kan manoma ya shige ni ne a lokacin da na fahimci yadda mawaƙan baka suke tsima manomanmu a lokacin da suke yi masu kiɗa tare da waƙa, har na fahimci kamar wani lokaci sukan fita hayyacinsu! Wannan abin ya burge ni sosai da sosai, don kuwa sai da har na fara shiga a ciki na ji yadda suke ji idan ana kiɗa masu gangar noma.

Da farko na ɗauka cewa ba abu ne mai sauƙi ba a ce mutum ya ɗauki manya-manyan waƙoƙi irin waɗannan ya haɗa su wuri ɗaya ya rubuta su, ga su cike da kalmomi da kalamai masu wahalar fahimta! Sai kuma wani tunanin ya shigo mani cewa idan ba a yi wannan aikin ba a daidai wannan lokacin wasu waƙoƙin na iya salwanta a duniya, wannan ya sa na yanke shawarar in zaɓi wasu waƙoƙin musamman waɗanda mafi yawan mutane suka sani don in kawo su a amfana da su. A dalilin haka ne na ga cewa ya kamata in kira wannan littafin da suna “Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Mawaƙan ba ka Na Noma”. An sha haɗuwa da matsaloli wajen a fahimci abin da mawaƙan suke cewa, kuma ga shi wasu sun yi nisa, ko kuma sun riga sun rasu! Ga kuma zamanin da ake ciki na matsalolin tsaro, waɗanda sukan kawo tarnaƙi ga tafiye-tafiye don a sadu da su a tantance su sosai, amma dai an yi ƙoƙarin a rubuta daidai, kuma da yardar Allah an yi abin a yaba.

Da yawa waɗansu waƙoƙin da masu su sun wuce ba a naɗe su ba ga na’u’rori! Waɗansun kuwa tafashe ne kurum don zaburad da manoma, sai wasu ‘yan kirare-kirare da akan haɗa su da su! Wasu kuma na sami waƙoƙin amma na kasa fahimtar kalmomin da mawaƙin ko ‘yan amshi ke faɗi a cikin ɗiyan waƙoƙinsu, kamar misali waƙoƙin makaɗa Garba Ɗanduddu Gangarak Kuryad Dambo da na Attah Dabai da wasu na Mande Dalli Bunguɗu. Yanzu dai sai a sha yadda aka dama inji Hausawa, wato a yi amfani da waɗanda aka samu, sai dai can gaba idan hali ya yi sai a ƙara gurgusawa.

Daga cikin hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanai akwai tuntuɓar wasu makaɗan waɗanda suke a raye, domin samun tarihin rayuwarsu tare da wasu ingantattun bayanai a kansu da kuma waƙoƙinsu, su kuma waɗanda suka riga mu gidan gaskiya, mun sadu da wasu yaransu da suka haifa, ko kuma yaransu da suka yi yawon kiɗin tare da su, ko ma wasu mutanen daban waɗanda suka san su tare da waƙoƙinsu, domin bayar da dukan bayanan da aka buƙata a kan mawaƙan ko waƙoƙinsu. saboda haka kafin a kawo waƙoƙin kowane mawaƙin an kawo taƙaitaccen tarihin rayuwarsa har da hoto ko hotunansa don a san shi kuma a gane shi, a kuma iya tantance shi.

Bayan wannan sai aka dubi wasu ayyukan da suka gabaci wannan a kan adabin Hausa musamman a ɓangaren waƙoƙin baka, domin a sami daidaita dukan waƙoƙin da aka samo daga mawaƙan, ko kuma gidajen rediyo ko daga wayoyin salular waɗansu ‘yan’uwa da abokan arziki, ko ta hannun masu sayar da kasa-kasan waƙoƙin Hausa.

Akwai wasu shahararrun makaɗan noma da watakila jama’a su dubi waƙoƙinsu a wannan littafin ba su gani ba, wato Mamman Amali Sububu da Mamman Nata’ukka. Wannan ta faru ne saboda na riga na rubuta littafi a kan rayuwarsu da waƙoƙinsu tun gabanin wannan littafin, don haka sai a nemi waɗannan littattafan idan ana buƙatar a san su da waƙoƙinsu.

A babi na farko na wannan littafin an kawo waƙoƙin manoma ne na mawaƙan da suke sanannun mawaƙan noma ne kurum, wato waɗanda a duk inda aka ji su ko waƙoƙinsu sai an tuna da noma, wasu ma daga cikinsu ba su taɓa yi wa wani abu waƙa ba in banda noma.

Sai a babi na biyu aka kawo wasu waƙoƙin irin waɗanda wasu mawaƙan suka yi wa manoma. Su waɗannan nau’in mawaƙan ba a cikin nau’in mawaƙan noma ba ne, suna da nasu waƙoƙin da aka san su da su kamar yadda manyan masana adabin Hausa suka rarrabe su.

Shi kuma babi na uku an kawo waƙoƙin da mawaƙan suka yi wa wani abu domin noma. Ma’ana a nan ba manoman suka yi wa waƙoƙin nasu ba kai tsaye, sai dai wasu abubuwa kamar gonaki ko ƙungiyoyi ko hukumomi da sauransu. 

A babi na huɗu na wannan littafin an kawo wata waƙa ne wadda wani bawan Allah ya yi ta noma, amma a wajen ƙasar Hausa. Ya yi waƙar ne a cikin harshen Hausa kuma kamar yadda sauran makaɗan suka yi domin su sa manoma su ƙara himma wajen noma.

A ƙarshe dukan waƙoƙin da aka kawo an saurare su ne, sannan aka rubuta su, ko kaitsaye daga mawaƙin ko daga na’urorin naɗar waƙoƙin,  babu ɗaya daga cikinsu wadda aka rubuta daga yadda wani ya rubuta nasa, ko a littafinsa ko kuma a wata takarda kowace iri, don haka ana bayar da haƙuri ga kura-kuran da za a iya gani a cikin littafin. Allah ya taimaka mana ya sa a amfana da shi. Amin.

Post a Comment

0 Comments