Ticker

6/recent/ticker-posts

Godiya - Daga Zababbun Wakokin Mawakan Baka Na Noma

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Godiya 

Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, mai iko a kan  kowa da komai, wanda ya ƙaddara in rubuta wannan littafi na Wasu Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Mawaƙan baka Na Noma. Ina godiya ga iyayena waɗanda suka tarbiyyantar da ni, suka kuma sa ni makarantu daban-daban na karatun addini da na boko. Suka kuma  ba ni ƙwarin guiwar tsayawa in yi karatun, Allah ya saka masu da mafificin alherinsa, amin. Ina kuma miƙa godiyata ga malamina Farfesa Yakubu Aliyu Gobir wato wanda ya duba wannan littafi tare da yin gyare-gyare a cikinsa, tare da bada shawarwari don ƙara inganta shi don ya zama abin amfani ga al’umma baki-ɗaya, Allah ya biya shi. Ina godiya ga Maimartaba Sarkin Fulanin Bunguɗu wato Alhaji Hassan Attahiru Bunguɗu wanda ya saba da ba ni ƙwarin guiwar tafiyar da harkokina na cigaba, ya kuma saba taya ni bincike na dukkan wani abu da ya ɗaure man kai, Allah ya biya shi. Ba zan manta da yayana Alhaji Bello Umar Bunguɗu ba, na gidan rediyon jihar Zamfara wanda ya taimaka mani wajen samo man wasu waƙoƙin da ba a samun su a kasuwa, na fitattun waƙoƙin mawaƙan baka na noma, na ji daɗi ƙwarai na kuma gode masa Allah ya saka da alheri. Ina kuma gode ma abokin aikina wato Bashir  Aliyu Tsafe wanda ya zama abokin tafiyata wajen yin bincikena, kuma a koyaushe cikin shiri yake na duk wani abu da na ce a yi don aikin ya tafi daidai, Allah ya saka masa da alherinsa, amin. Sai kuma godiya ga malam Aliyu Abubakar Kanoma da Abdullahi Muhammad Birnin Magaji na gidan rediyon jihar Zamfara da kuma Mujitaba Ibrahim na gidan rediyon Rima na jihar Sakkwato domin sun taimaka mani matuƙa da wasu waƙoƙin noma, tare kuma da ba ni shawarwari don ƙarin ingancin aikina. Ina godiya Allah ya biya su baki-ɗaya. 

Post a Comment

0 Comments