Ticker

6/recent/ticker-posts

“Mu Tai Bara”.

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Mu Tai Bara”.

 Jagora: Mu tai bara don Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Ku taimaka don Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Allah sa muje gida dan Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Allah kare tsautse da Asara,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: A bamu domin Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Wa za ya bamu na Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Na zo don in samu,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Ku taimaka ku bamu,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Allah ƙara wa iyaye daraja,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Muje gida lafiya,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Mu cimma mutanen gida lafiya,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Kai mai sadaka Allah ya saka,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: To ina bara don Allah,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Allah ƙara wa iyaye daraja,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora: Allah ya kare tsautsayi da Asara,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Jagora; Wa zai ba guragu sadaka,

 Amshi: Saboda Manzon Allah.

 Ita kuwa wannan waƙar in an lura bara ne tsagwaronsa ba tare da surka waƙar da wani bege ba. Ita ma a cikin taro mabarata ke amfani da ita. A mafi yawan lokuta ƙungiyar mabarata da ke amfani da wannan waƙar takan haɗa masu naƙasa dabam-daban, kamar kutare da makafi da guragu da ma wasu gajiyayyu waɗanda ba su da wata naƙasa. Ita ma wannan waƙar wani daga cikin mabaratan ke bayarwa saura na amsa masa. Ga kuma wata mai suna Maula ta Sidi:

Post a Comment

0 Comments