Ticker

6/recent/ticker-posts

Maula Ta Sidi

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Maula Ta Sidi

 Jagora: Maula ta Sidi maula ta Balarabe.

Amshi: Maula.

Jagora: Babban gida da daɗin bara yake.

Amshi: Maula.

Jagora: Waccan ta ba ka waccan ta daɗa maka.

Amshi: Maula.

Jagora: Waccan ta ɗauki kere na shirin bugu.

Amshi: Maula.

Jagora: In ba ki ba ni shafa mani lahiya.

Amshi: Maula.

Jagora: In kin buge ni wallahi kina biya.

Amshi: Maula.

(Maula)

Wannan waƙar Gardawa suka fi amfani da ita wajen bara. Wato mabarata masu neman ilmi waɗanda suke sun wuce almajirci. Masu wannan waƙa ba su shiga cikin gidaje a lokacin da suke baran kamar yadda Almajirai ke yi, saboda su manya ne. A garkar gida suke tsayawa suna baransu ana aiko yara suna kawo masu sadaka. Ita ma a cikin taro ake rera ta, wani na bayarwa saura na amsawa. Mafi yawa ba kulium Gardawa ke fita wajen bara ba, sukan keɓe daren Jum’a da safiyarta domin yin bara. Wato ke nan tsarin baran nasu sati-sati ne.

Post a Comment

0 Comments