Ticker

6/recent/ticker-posts

Mu koma Gona

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mu koma Gona

  G/Waƙa: Haba yara mu koma gona.

 

  Jagora: Duk wani mai ƙodogo,

: Bai ban tsoro,

 

  Jagora: Mai gudun[1] gangan noma,

: Ban kula da wofi ba.

Jagora: Allah na ruwa,

: Kuma ƙasatana shanyewa,

 

Jagora: Mu dawo a baya nan.

 

Jagora: Allah jiƙan

: Sarkin noman Ningi.

 

Jagora: Sha baƙi magajin Abdu,

: A Duna gurun Findi.

: Uban Kasuwa uban Nahawo,

: Sarki Uba ga Bara,

 

Jagora: Allah jiƙan sarkin noma Dabo

: A gwayan.

 

Jagora: Dabo ɗan Dabo goyon manya.

: Ya bani girken zaki[2],

: Ga tauri ya bani,

 

Jagora: Na gangaro na tuna da Bazata,

 

Jagora: Kuma na tuna da Bazata,

 

Jagora: Amman nai babbam mantuwa,

: Nai babbam mantuwa,

 

Jagora: Tanko na Manu Barden haɓe

 

Jagora: Mai arziki a bakin karo na manu,

 

Jagora: Ka ga dubu na gona dubu na kurmi,

 

Jagora: Shi ma ya taɓa kaɗan ya kau,

 

Jagora: Mu yi tunani,

: Mu kai samame gonar Tanko.

: Na gode taimako ɗan Tanko

Jagora: Yai sarautar sarkin noma shi ma,

 

Jagora: Ku tuna da baya fa,

 

Jagora: Akwai Dallami a Gwayan,

 

Jagora: Wo Dallami a Gwayan

 

Jagora: Ɗan Idi baban Idi,

: Dallati a Gwayan.

 

Jagora: Sarakan noma,

: Gasu nan iri-iri ne,

 

Jagora: Wani sarkin noma,

: To biri da wando.

 

Jagora: Wani sarkin noma,

: Sha lissafin manoma.

 

Jagora: Amman nai tunanin za ni je,

 

 Jagora: Garin su Gaga,

: Bala na Gaga.

 

Jagora: Ɗan Hadiza ɗan Mairiga,

 

Jagora: Shi ma yai sarkin noma.

 

Jagora: Wai ina Burdume ya dawo?

Jagora: Wai ina Burdume sai wata rana,

 

Jagora: Allah jiƙan sarkin noma Ibrahim.

 

Jagora: Zubin Halilu ba zubin banza ba.

 

Jagora: Ɗan Idi baban Idi Dallati a Gwayan.

 

Jagora: Dagan an na wuce sama gani nan,

 

Jagora: Allah ya kai ni Gagar tsakuwa.x2

 

Jagora: Ga rumbun tuwo ga rumbun kuɗi.

 

Jagora: Uban Sulemanu uban Charki,

 

Jagora: Sarki uban Sulemanu.

 

Jagora: To mu je mu zuga su,

 

Jagora: Allah jiƙan sarkin noma Ayuba.

 

Jagora: Uban Dogara baban Karimu

 

Jagora: Gaji mai nama na Gwandara,

 

Jagora: Gaji ɗan Ibrahim na Gwandara.



[1]  Raggo kenan wanda bai iya yin noma.

[2]  Wata rig ace mai ƙawa sosai.

Post a Comment

0 Comments