Ticker

6/recent/ticker-posts

Dauduwa Keffi Sarkin Makadan Noma na Jihar Nasarawa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Dauduwa Keffi Sarkin Makaɗan Noma na Jihar Nasarawa

Ga dukan alama makaɗin ba Bahaushe ba ne, na yi tunanin in kawo shi da waƙar noman tasa saboda harshen Hausa yake amfani da shi wajen waƙar, kuma ta noma ce.  

Dauduwa Keffi Sarkin Makaɗan Noma na Jihar Nasarawa

Shi wannan makaɗn noman ya sha bamban da sauran saboda shi kaɗai yake yin waƙarsa, sai Ɗan ma’abbansa wanda yakan ja zaren tunaninsa a cikin waƙar. Sannan kuma bayan gangarsa ta kiɗin noma wadda akwai mai kiɗa masa ita, shi kuma da tasa wadda idan ya ga dama yake kiɗawa, akwai wani mabushi da yake da shi wanda suke tare wanda yake yi masa busa, ita busar ita ke zama tamkar amshi a waƙar tasa.

Dauduwa Keffi Sarkin Makaɗan Noma na Jihar Nasarawa

Post a Comment

0 Comments