Ticker

6/recent/ticker-posts

Kammalawa - Daga ZKunshiyar Littafin Zababbun Wakokin Mawakan Baka Na Noma

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Kammalawa

Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin sarki wanda ya kawo mu wannan lokaci na kammala rubutun wannan littafi na waƙoƙin noma wanda makaɗan Hausa suka yi. An kalli waƙoƙin mawaƙan baka na Hausa iri daban-daban da aka yi na noma, An kuma kalli mawaƙan ba ka daban-daban waɗanda suka yi wa manoma ko kuma wasu abubuwa don noman. Alal misali wasu sun yi wa gonakin noma waƙar, wasu ƙungiyoyin manoma wasu kuma sun yi wa gandun daji da sauransu. A taƙaice dai dukkan waƙoƙin da suke da nasaba da noma su ne aka zaƙulo don a taskace su a sami abin da za a iya amfani da shi a gaba.

 

Ba a kawo waƙoƙin wasu sanannun makaɗan noma su biyu ba a wannan littafin, saboda dalilin cewa na riga na rubuta littafi a kan kowane ɗaya daga cikinsu, inda na bayyana tarihin rayuwarsa da kuma waƙoƙinsa. Mawaƙan su ne Mamman Amali Sububu da kuma Mamman Nata’ukka Gandasamu. Don haka duk mai neman wani abu a kansu ko waƙoƙinsu ya nemi waɗannan littattafan.

 

Daga cikin mawaƙan da aka kawo waƙoƙinsu akwai Daudun kiɗi Jambaƙo da Alhaji Abu Ɗankurma Maru da Alhaji Mamman Shata da makaɗa Sa’idu Maidaji Sabonbirni da Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Makaɗa Audu Ɗangunduwa Kagaram Morai da Sani Sabulu da Ɗanbalade Morai da Bawa Ɗan’anace da Illon Kalgo sai kallabi tsakanin rawunna wato Hauwa Kulu Mukkunu. Haka kuma akwai Abdullahi Ɗanɓurji Morai da Alhaji Shehu Ajilo Ɗanguzuri da Alhaji Sani Ɗan’indo da Alhaji Idi Loga da Baƙo Rugum Ƙiri da kuma Sale Sarkin makaɗan Maimartaba Sarkin Fulanin Bunguɗu.

 

Sauran makaɗan noma waɗanda ba a sami kawo waƙoƙinsu ba saboda wasu matsaloli kamar yadda na ambata wajen gabatarwar wannan littafin sun haɗa da makaɗa Mande Dalli Bunguɗu da makaɗa Attah Dabai da makaɗa Hamza Satiru da Makaɗa Garba Ɗanduddu Gangarak Kuryad Dambo da makaɗa Karɓau Ƙauran Namoda da dai sauran shahararrun makaɗan noma na ƙasar Hausa. Da fatan za a yi mani uzuri sai wata dama ta sake samuwa a taɓo su baki-ɗaya.

Post a Comment

0 Comments