Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Mu Gode Allahu Mai Rahama: Ta Malam Zainu Zubairu Bunguɗu
1. Mu gode Allahu Mai Rahama,
Rahamarsa bai
manta kowa ba.
2. Tsira ta dawwama ga manzonsa,
Dukansu ba’a keɓe kowa ba,
3. Zuwansa yazan zuwan rahama,
Garemu ba ko da
nisa ba.
4. Alaye Sahabbai Iyalansa,
Zuriyarsa ban zaɓe kowa ba.
5. Da Malamai masu bin sunnah,
Ban ce da wannan ƙazami ba.
6. Allahu na roƙi ilhami,
Gareka ba don isa
ta ba.
7. Don shugabanmu macecinmu,
Wannan da bai taɓa laifi ba.
8. Shi ya fi kowa wajen daraja,
Tausai ba ai ba
kamarshi ba.
9. Baiwa na zo karya kafirai,
Zuwansa ba su
sheda daɗi ba.
10. Da Larabawa da baubayi,
Ba a samu gwarzo
kamar shi ba.
11. Ba a haifi ɗa mai sifatai ba,
Ba za’a haifi awar
shi ba.
12. Madogarar masu addini,
Islamiyya ba mishawa
ba.
13. Aminu Sadiƙul Masduƙu,
Ba a samu mai
gaskiyatai ba.
14. Mu tattaro mu bi Allahu,
Ba a yo mu don
shagali ɗai ba.
15. Allahu ya yomu don bauta,
Bai yo mu don
bauta banza ba.
16. Jama’a mu bauta ma Allahu,
Bai ce mu bauta
wani nai ba.
17. A ɗau zancen huwa Allahu,
Kalmag ga ba ta ba
da fili ba.
18. Kowa da manzo wujibina,
Ban ce ga kalmar
khususiya ba.
19. Ma a ti kumdubi baɗato,
Bayar da yinta da
wasa ba.
20. Neman sani farlu aini ne,
Tsakalaini ba a keɓe kowa ba.
21. Tardi da sunnah da wajibi,
Ba a sauƙaƙa su ga kowa
ba.
22. Duba ga zance hi wallahu,
Bai keɓe kowa ga dibi ba.
23. Fasalu ahlazzikiri,
Duba ta butu baka
filiba.
24. Musan huwallahu shi ne ɗai,
Zagi siga bada
tsaniya ba.
25. Shi ya yi kome da kowa duka,
Bai tara komi da
kowa ba.
26. Hakan ga bauta mu bauta mai,
Bai tara mulki da
kowa ba.
27. Shi ka shikai na ibada to,
Guda biyar ba da
waiba.
28. Shahada taini kaza sallah,
Ƙidansu bai zo da nauyi ba.
29. Azumi da zakka sako hajji,
Rufesu bako da
wargiba.
30. Dan babu wasa ga addini,
Zancen ga bai zan
fadata ba.
31. Wanka na tsarki wajibi na,
Ga baligi ba ga
kowa ba.
32. Ko yaushe janaba ta same ka,
Wanka kake ba da
nayyi ba.
33. Taro mazanmu da matanmu,
Haɗa sagir ba a keɓe kowa ba.
34. Haila nifasi ga matanmu,
Ba a sauƙaƙa ta ga kowa
ba.
35. Tardi kudu’i ga mai sallah,
Shi yi taimama ba
wudu’i ba.
36. Sai wanda ya zan,
Mulkinsa bai rage
kowa ba.
37. Mu bauta Allahu mai ƙudura,
Bai ɓata ƙarfinsa banza ba.
38. Ko wabbi Allahu ya huta,
Dimma sun bi bada
wargi ba.
39. Janfansu na can ya tara,
Ba a hori kowa da
bina ba.
40. Mukama sunnah mu bar bidi’ah,
Bai bauta mai
bashi komai ba.
41. Kowabbar bautarsa ya taɓe,
Bautar ko ba ta
duba komi ba.
42. Ku bauta banza kuzan banza,
Mazanmu basu shafi
kowa ba.
43. Mai tasbahal hajji inna,
Dikinka bai kare
kowa ba.
44. Dumaso shatu da mai sufi,
Aikinka bai zan da
shiriya ba.
45. Ƙarya namima munafunci,
Mai yinsu ba za
shi tsira ba.
46. Daci da ceto da kha’inci,
Mai yinsu ba za
shi tsira ba.
47. Haka shangiya yi da girman
kai,
Mai yinsu baza shi
tsira ba.
48. Mu daina ƙwace mu bar fahara,
Mai yinsu ba za
shi tsira ba.
49. Da mai halatta haramiya,
Wallahi ba za shi
tsira ba.
50. Da mai haramta halaliya,
Guzurinsa ba za a
karɓa ba.
51. Da cin gululi zalinci,
Mai yinshi ba zai
tsira ba.
52. Haka nan riyar mu bar yinta,
Mai yinta ba zai
tsira ba.
53. Da dukiyar wanda bai da uba,
Kwacci ta ba za
shi tsira ba.
54. Mai cin amana da iskanci,
Mai yinshi ba za
shi tsira ba.
55. Da masu murna da kafirci,
Murnassu bata da ɗa komi ba.
56. Kukansu na tsana an tara,
Guzurinsu bai zan
nasheshi ba.
57. Sai wanda ya tuba ya daina,
Ba za a tuna hali
nai ba.
58. Allahu yay muna alkawali,
Ba za shi swaɓa faɗatai ba.
59. Komi kake so kana samu,
Ni’i marta ba zata
kare ba.
60. Ga kautsara salsalibu mu sha,
Daɗinsa bamai iyaka ba.
61. Akwai gurasa akwai cincin,
Da na kiya ba da
nisa ba.
62. Akwai halawa dama,
Da kin-kin bana
tuya ba.
63. Aljanna shayi da alkuskus,
Ba wagga suya ta
mata ba.
64. Nama dafaffe da soyayye,
Ni’imat ta ba za
ta ƙaura ba.
65. Nama na kifi da tsuntsaye,
Da marmari ba na
yinwa ba.
66. Diyan itace da alkaki,
Ga ɗakina ba na bunu ba.
67. Ga kasiratu suna murna,
Angonsu bai zo
gadaje ba.
68. Haskensu ya wuce haske duk,
Ƙawarsu ba ta ɓoye bargo ba.
69. Ƙamshinsu yasina almiski,
Tabshinsu ba zai
misaltu ba.
70. Da shimfiɗu da gadajensu,
Da majingini bana
rimi ba.
71. Kuma ga kujeru na kin tayakin,
Kafinta bai haɗa koɗai ba.
72. Zinariya wa su murjani,
Ƙawarsu bata zan kama ɗai ba.
73. Da Lu’u-lu’u wasu di baji,
Aljanna ba ta zan
kama ɗai ba.
74. Wato tabna harzuƙa da faɗa,
Ga munafukai ba da
rauniya ba.
75. Duk hankalin kafirai shi ɓace,
Sun hangi ba zasu
tsira ba.
76. Son zuciya sunka tasamma,
Sun zaɓi yau basu farko ba.
77. Kowabbi son zuciya nan,
Halakarsu ba zata
nau yi ba.
77. Biyar ta zaɓin gidan halaka,
Hajjimmu ba zata
sauna ba.
78. Ita kurkuku ce ga mai binta,
Zaɓin ta bai bar ka shirya ba.
79. Zabaniyawa su kama shi,
Duka suke ba da
wargi ba.
80. Su basu saɓa faɗar Allah,
Ko ƙanƙane ba kamar mu
ba.
81. Duk wanda yaƙi umurninta,
Ba zai ga wannan
misibar ba.
82. Man khafa rabbahu ya huta,
Munarsa ba a san
iyaka ba.
83. Aljanna can zashi ba fashi,
Wa’adinsa ba za
shi tayar ba.
84. Aljanna daɗinta ya fi gida,
Daɗinta ba a san iyaka ba.
85. Gulbin ruwa wanda ya fi zuma,
Zaƙinsa ba a san iyaka ba.
86. Gulbin zuma madara da giya,
Ka shata ba zaka
maye ba.
87. Kuma ga azurta da marjani,
Sifarta ba zata
ganu ba.
88. Akwai tufafi iri da iri,
Ba a san iyakar ƙawa tai ba.
89. Akwai awaki da raƙuma,
Aljanna ba za mu
tsufa ba.
90. Ba mai tunani da zai mutuwa,
Abadan ba zai sake
ƙaura ba.
91. Da babu ciwo ciki abada,
N’imarta ba zata
tsufa ba.
92. Matansu ba wadda ke haila,
Bare ace bata yo
tsarki ba.
93. Haka ba nifasi ga Aljanna,
Shagali suke ba da
ƙoshi ba.
94. Kuma ba turoso bare bauli,
Ko kaci ba zaka
khabasi ba.
95. Aljanna ba majinar hanci,
Sai kwalliya ba ƙazamta ba.
96. Aljanna daɗinta ya fi gida,
Ni’imarta ba za ta
gamu ba.
97. Ya rabbi yafe zunubbaina,
Dukkansu ba don
halina ba.
98. Ya rabbi saukar da jinƙanka,
Garemu ba don
halina ba.
99. Kuka nike Nawa laifuka,
Da na yi ban san
iyaka ba.
100. Ƙanana sun fi dubu miliyan,
Ban ƙirga laifin dana yo ba.
101. Manyansu sun fi ƙanana yawa,
Ba zan gane halina
ba.
102. Halin da na yi babu kyawo,
Ba zani manta
halina ba.
103. Saɓo nike bani fasawa,
Kullin daɗi ba da rauni ba.
104. Tuna shi kan sani yin kuka,
Halinga bai bani
sha’awa ba.
105. Allahu na roƙi jin ƙanka,
Ka bamu si ba da
nisa ba.
106. Rahamarka tafi zunubai na,
Jinƙanka bai rage kowa ba.
107. Wanke ni in zama tsarkaka,
Islamu ba fa
niyyarka lama ba.
108. Ya rabbana bamu jinƙanka,
Mu san shiga ba da
wargi ba.
109. Ya rabbana yafe laifinmu,
Tun ba a kira mu
zuwa can ba.
110. Ka yafe laifin da mun gwabza,
Mu tsira tun ba da
ƙuna ba.
111. Diyanmu tare da matanmu,
Da ɗiyansu ban keɓe kowa ba.
112. Da ‘yan uwana masoya na,
Islamu ba kafirawa
ba.
113. Musa dawwama cikin ni’ima,
Ni’imar da ba zata
ƙare ba.
114. Ba don halinmu da cikinmu,
Dumma su bi ba da
wargi ba.
115. Domin sahabbai da alaye,
Musa mu kai ba da
suna ba.
116. Da sussuka daɗa tai tsaba,
Aljannah bamu ƙuna da haushi ba.
117. Wa’azi nike gani ba ilimi,
Kuma jahili ba
cikakke ba.
118. Ya malamaina ku dube ni,
Ku yi taimako ba
da wargi ba.
119. Na roƙi gyara ga malumma,
Na gaskiya ba
mishawa ba.
120. In sun kace maka wai waƙa,
Ɗan malami bada fahari ba.
121. Zubairu Bunguɗu babansa,
Sunansa bai zan ɓatacce ba.
122. Uwarsa Aisha ‘yar Malam,
Sayuɗi ban ɓoye komai ba.
123. Ismi Muhammad Ɗan Malam,
Zubairu ban raɓa laƙabi ba.
124. Bare kace zaka neme ni,
Ka kaini ba inda
na kai ba.
125. Baiti ɗari munka ƙirga ta,
Saba’in suna bi
bila rai ba.
126. Sannan takwas sunka raɓo su,
Bayansu bai ƙara komi ba.
127 Hijira ɗafin sahi na yi ta,
Ɗakin rajab ba da ɓaci ba.
128. Tammat Wa amnat bi aunillahi,
Rabil wara ba wani
na ba.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.