Ticker

6/recent/ticker-posts

Bani Malam

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

Bani Malam

 Jagora: Bani Malam,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Fi sabilil lahi,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Don girman Allah,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Saboda Rasulullahi,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Annabi ɗan Abdullahi,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Kowa ya baiwa makaho,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Ya bai wa Rasulullahi,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Alhaji wa yai niyya,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Ya bai wa Rasulullahi,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Ke ‘yar jagora,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Je ki karɓo sadaka,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Allah ya biya da buƙata,

 Amshi: Bani Malam.

 Jagora: Ya kai gidan aljanna,

 Amshi: Bani Malam.

Post a Comment

0 Comments