Ticker

6/recent/ticker-posts

Wacce Irin Rantsuwa Ce Ke Wajabta Yin Kaffara?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, don Allah ina so ayi min cikakken bayani akan irin rantsuwar da take wajabta kaffara, saboda an maida ta kamar al'ada cikin al'umma, wallahi kaza wallahi kaza, Meye cikakken bayaninta? ngd.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Ba kowace rantsuwa ce take wajabta yin kaffara ba, rantsuwar da take wajabta yin kaffara ita ce rantsuwar da aka yi ta da nufi, mutumin da ba a san shi da yawan rantse-rantse a maganganunsa ba, sai kawai yana cikin magana sai ya ƙarfafa maganarsa da yin rantsuwa da nufinsa har zuci, to matuƙar bai aikata wannan abin da ya rantse a kansa ba, to kaffara ta wajaba a kansa.

Amma idan mutum mai yawan rantse-rantse ne a zantuttukansa, ta zama masa al'ada a cikin maganganunsa na yau da kullum, duk wata magana da zai yi sai ya haɗa ta da rantsuwa, kamar mutum ya ce: "wallahi yanzu na dawo, wallahi da muka je garin su wane, ba zan sha ba wallahi, wallahi kai dai a yi sha'ani kurum",  irin wannan rantsuwa ita ce ake kira YAMINUL LAG'WI, mai yin wannan ya mayar da ita al'ada a maganganunsa, to Allah ba ya kama bayinsa da irin wannan rantsuwa, wato ba ta wajabta yin kaffara, kamar yadda Allah S. W.T ya bayyana a farkon aya ta 89 da ke suratul Ma'ida:

لَا يُؤَاخِذُكُمُ اللَّهُ بِاللَّغْوِ فِي أَيْمَانِكُمْ وَلَٰكِنْ يُؤَاخِذُكُمْ بِمَا عَقَّدْتُمُ الْأَيْمَانَ ۖ فَكَفَّارَتُهُ إِطْعَامُ عَشَرَةِ مَسَاكِينَ مِنْ أَوْسَطِ مَا تُطْعِمُونَ أَهْلِيكُمْ أَوْ كِسْوَتُهُمْ أَوْ تَحْرِيرُ رَقَبَةٍ ۖ فَمَنْ لَمْ يَجِدْ فَصِيَامُ ثَلَاثَةِ أَيَّامٍ ۚ ذَٰلِكَ كَفَّارَةُ أَيْمَانِكُمْ إِذَا حَلَفْتُمْ ۚ وَاحْفَظُوا أَيْمَانَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Allah bã Ya kãmã ku sabõda yãsassa a cikin rantsuwõyinku, kuma amma Yanã kãmã ku da abin da kuka ƙudurta rantsuwõyi (a kansa). To, kaffãrarsa ita ce ciyar da miskĩni gõma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyãlanku, kõ kuwa tufãtar da su, kõ kuwa ´yantãwar wuya. Sa'anan wanda bai sãmu ba, sai azumin kwãna uku. Wannan ne kaffãrar rantsuwõyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyãye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ãyoyinsa, tsammãninku kunã gõdewa. (Suratul-Má'ida 89)

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments