Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Shagon Bachirawa

"Dubi tsayin ga na Shagon Bachirawa,
Kamar dokin sukuwa in an yi zama
A yi gwa-da-gwa da kai aƙ ƙarya
Kwac ce ya tsaya maka wannan ya yi ƙarya. 
Shago da yash shiga Legas dambe
Ga randa zaki yaz zaka filin dambe
Na ga Kudawa sun gama kanu
Ce duk su shira maka Shago dambe kaz zo
Ai Salisun Wada mu kausai
Shi ma ya hwaɗi tsakanin 'yan uwa nai
Yara ina Ramarega yay yi? 
Shi ma ya hwaɗi tsakanin ƴ'yan uwa nai
Alfa Bayarabe mun kausai
Alfa na gan shi da gari an jiƙo mai
Yan yara Maitala nika kallo
Shi ma ya hwaɗi tsakanin ƴan uwa nai" 

–Marigayi makaɗa Alhaji Mamman Maiturare Wababe

Daga Zauren:
Makaɗa Da Mawaƙa

Post a Comment

0 Comments