Ticker

6/recent/ticker-posts

Marigayi Malam Tagwai Sambo

Marigayi Malam Tagwai Sambo
A cikin wata Waƙar Marigayi Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Muhammadu Bashar Uban Kiɗi ya na ambatar wannan bawan Allah, Marigayi Malam Tagwai Sambo a lokacin ya na da wannan Muƙami na Kwamishina a Tsohuwar Jihar Arewa Ta Tsakiya (North Central State, Kaduna da Katsina na yau kenan) bai zamo Sarkin Moroa ba, watau bai gadi gidan su ba a lokacin.

A cikin Waƙar Uban Kiɗi ya na bayyana zuwan sa Daura a matsayin babban baƙo wajen bikin miƙa Takobin Girma wanda Yankin Daura ya yi ta lashewa har sau uku a gasar gudanar da ayyukan gayya da ƙungiyoyin gama kai da taimakon juna duk a faɗin Jihar ta Arewa Ta Tsakiya.

A cikin Waƙar dai Uban Kiɗi ya na fitowa da ƙwazon Marigayi Mai Martaba Sarki a irin waɗan nan ayyukan. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments