Ticker

6/recent/ticker-posts

Mani

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mani

 

  G/Waƙa: Ya taho wurin noma,

: Za ni in gaida Mani.

  Jagora: Ya taho wurin noma,

: Za ni in gaida Mani.

‘Y/ Amshi: Ya taho wurin noma,

: Za ni in gaida Mani.

 

  Jagora: Salame nit taho,

‘Y/ Amshi: Mani ya biya ya yi girma.

 

Jagora: Salame zan kiɗi,

 ‘Y/ Amshi: Mani ya biya ya yi girma,

: Ya taho wurin noma,

: Za ni in gaida Mani.

 

Jagora: ‘Yan Salame su ka noma,

‘Y/ Amshi: Mai ba mu ge,

: Ro ina damu,

 

Jagora: ‘Yan Salame ba Bahili

 ‘Y/ Amshi: Ai kowat taho sais u cisai

 

Jagora: Adamu kun biya kiɗi,

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara ma girma,

 

  Jagora: Muhammadu kun biya kiɗi,

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙarama girma.

 

Jagora: Ɗiyan Ɗantakati kun biya,

 ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara ma girma

 

  Jagora: Jikan Rabe ba bahili,

‘Y/ Amshi: Yau kowat taho sai ya cisai.

: Ya taho wurin noma,

: Za ni in gaida Mani.

 

 Jagora: Allah shi ka yin rabo

 ‘Y/ Amshi: Sai ya ba ka ya ba ka girma...

 

 Jagora: Kai gahwarakka Yaroi

 ‘Y/ Amshi: Ai kisai

 

Jagora: Allah shi ka yin ruwa,

‘Y/ Amshi: Ai shikka a zan tar da gero.

: Ya taho wurin noma,

: Za ni in gaida Mani.

 

  Jagora: A aza ma raƙumii,

‘Y/ Amshi: Kaya bai kamance da jaki.

Post a Comment

0 Comments