Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Arzikin Hatci Haruna

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mai Arzikin Hatci Haruna

 

 G/Waƙa: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba shi yunwa..

 

Jagora: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba shi yunwa.

‘Y/ Amshi: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba ka yunwa.

 

  Jagora: Amma Ɗankado can gidan Bashar dai,

‘Y/ Amshi: Kowag  gane su ba shi yunwa.

 

Jagora: Goga,

‘Y/ Amshi: Kowag  gane su ya wadata.

: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba shi yunwa.

 

Jagora: Ka san motocin ƙwarai garai Haruna,

: Gero hatci gami da dawa.

 ‘Y/ Amshi: Kowag gane su ya wadata,

 

  Jagora: Goga,

‘Y/ Amshi: Kowag  gane su ya wadata.

: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba ka yunwa.

 

  Jagora: Amma in zo kiɗi gida Bashar ne,

: Ɗan Musa abin biya ga daji

: Gero shina gidan Bashar dai

‘Y/ Amshi: Dawa tana gidan Bashair ne,

 

Jagora: Kun san….

 ‘Y/ Amshi: Wake yana gidan Badar ne,

 

  Jagora: Kun san..

‘Y/ Amshi: Maiwa tana gidan Badar ne,

 

Jagora: Sannan masara …,

‘Y/ Amshi: Tana gidan Badar ne..

 

Jagora: Sannan gujiya …,

‘Y/ Amshi: Tana gidan Badar ne..

 

Jagora: Shinkakwa…,

‘Y/ Amshi: Tana gidan Badar ne..

 

Jagora: Sannan alkama,

‘Y/ Amshi: Tana gidan Badar ne..

 

Jagora: Sannan komi ka so …,

‘Y/ Amshi: Gidan Badar ne..

: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba shi yunwa.

 

Jagora: Amma Ɗan Ummaru ya biya gareni,

: Ɗan Ummaru Ɗan Audu mai halin mu gode,

: Ɗan Garba mai hura da nono…,

 ‘Y/ Amshi: In nig gane shi ba ni yunwa.

 

Jagora: Ni dai,

‘Y/ Amshi: Ni ko abinci ba ni yunwa.

: Mai arzikin hatci Haruna,

: Kowag gane shi ba shi yunwa.

Post a Comment

0 Comments