Ticker

6/recent/ticker-posts

Mamman Dankyauta

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mamman Ɗankyauta

G/Waƙa: Ɗan mazana bai huta ba,

: Mai kuge gojen Ɗankyauta.

 

  Jagora: Mu koma zuwa ga noma.

  ‘Y/ Amshi: Tashi mu koma zuwa ga noma,

: Bai ƙare ba.

: Da baza ta ban canza ba.

 

  Jagora: Ko gobe mai gidana.

  ‘Y/ Amshi: Amadu ko gobe mai gidana.

 

  Jagora: Amadu ko gobe mai gidana.

  ‘Y/ Amshi: Amadu ko gobe mai gidana,

: Bai huta ba.

 

  Jagora: Ga dangalinku mutan Nasarawa.

  ‘Y/ Amshi: Ga dangalinku mutanen Rabe,

: Na waje na bai huta ba.

 

  Jagora: Nazo kiɗi gidan Mamman Ɗan kyauta,

: Na iske inda dame yat taru,

: Akwai hatci nan sunas suna,

: Na sha hura na ba dokina,

: Na ci tuwo na ba ‘yan yara.

  ‘Y/ Amshi: Hattara ku kau ‘yan yara,

: Ban iya wargin yasoso ba.

 

  Jagora: Koda hattara  ku kau yan yara.

  ‘Y/ Amshi: Ban iya wargin wasoso ba.

: Ɗan mazana bai zauna ba.

 

  Jagora: Nazo kiɗi gidan Mamman ɗan kyauta,

: Na iske inda dame yat taru,

: Na ga hatsi nan sunas suna,

: Na sha hura na ba dokina,

: Na ci tuwo na ba ‘yan yara.

: Hattara ku kau ‘yan yara,

: Ban iya wargin yasoso ba.

: Ɗan mazana bai huta ba,

: Mai kuge gojen Ɗankyauta.

  ‘Y/ Amshi: Hattara ku kau yan yara,

: Ban iya wargin yasoso ba.

: Ɗan mazana bai huta ba,

: Mai kuge gojen Ɗankyauta.

 

Jagora: Haba kai da ko baki gare ka ko inama.

  ‘Y/ Amshi: To ko baki gare ka yafi  shahe-zane.

 

  Jagora: Mai riga da dashi yai aure,

  ‘Y/ Amshi: A ban kuɗina in sai riga.

: Ko dauri angonci ni zan yi.

 

  Jagora: Yana kiɗi tsahoki na tasowa.

  ‘Y/ Amshi: Na gidana bai huta ba.

 

  Jagora: Mu koma zuwa ga noma.

  ‘Y/ Amshi: Tashi mu koma zuwa ga noma,

: Bai ƙare ba.

Post a Comment

0 Comments