Ticker

6/recent/ticker-posts

Mamman Dangandau

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Mamman Ɗangandau

 

G/Waƙa: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa[1].

 

  Jagora: Bawa Allah waddan karen aro.

  ‘Y/ Amshi: An tahi ba a dawo da shi gida ba.

 

  Jagora: Bawa Allah waddan karen aro.

  ‘Y/ Amshi: An tahi ba a dawo da shi gida ba.

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

  Jagora: Gaishe ka na maidawa.

  ‘Y/ Amshi: Mai yo ma hakin daji zahi-zahi.

 

  Jagora: Damana ta ɗingimta.

  ‘Y/ Amshi: Damana ta ɗingimta ai ta noma.

: A kashe raggo a bag gani nai.

 

  Jagora: Kun san na bas shiri da shi.

  ‘Y/ Amshi: Na ce jaƙ ƙaniyau uwatai.

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

  Jagora: Damana ta ɗingimta.

  ‘Y/ Amshi: Ai ta noma,

: A kashe raggo a bag gani nai.

 

  Jagora: Gaishe ka na Maidawa.x2

  ‘Y/ Amshi: Ɗan maza

: Mai yo ma hakin daji zahi-zahi.x2

 

  Jagora: Don dai kar ka bari swahiya ta waye.

  ‘Y/ Amshi: Kyawon noma a zanka[2] sabko.

Jagora: Kai dai kar ka bari swahiya ta waye.

  ‘Y/ Amshi: Kyawon noma a zanka sabko.

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

  Jagora: Haba ku bari in munka zo mu gona,

‘Y/ Amshi: Shi mai ƙarhi akwai wurinai,

: Sai ba a kawo ga kakare ba,

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

  Jagora: Ɗan maza ban ce ka ji tsoron.

  ‘Y/ Amshi: Ɗan maza ban ce ka ji tsoron biɗah hatci ba.

 

  Jagora: Mamman ya yo ɗari na gero,

: Kana ya yo ɗari na maiwa,

: To kuma ya yo ɗari na dawa

: Ko dajanjare.

 

  ‘Y/ Amshi: Ko da janjare ita da ab ban…

: Za metin anka mulmulo mai.

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

  Jagora: Gaishe ka na Maidawa.

  ‘Y/ Amshi: Ɗan maza,

: Mai yo ma hakin daji zahi-zahi.

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

 Jagora: Muhammadu Ɗanmanau,

: Munka zo mu noma,

: Yak kau ɗebo kuyye Talata,

: Har Ranai sunka zo su kallo.

  ‘Y/ Amshi: Ko kahin swahiya ta waye,

: Mamman ya kai su Dangazori,

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.

 

 Jagora: Kyawon noma a zanka sabko.

‘Y/ Amshi: Kyawon nomad a dungu-dungu.

: Ɗangandau Ɗan Ubandawaki,

: Mamman ya gota ‘yanbanawa.



[1]  Samari kenan, Babane tilo. Saurayi kenan.

[2]  Riƙa yin abu.

Post a Comment

0 Comments