Ticker

6/recent/ticker-posts

Abdulkarimu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Abdulkarimu

A garin Maɗwacci ne Abdulkarimu yake, na yamma ga Rini ta ƙaramar hukumar Bakura. Ya shahara da noma na hatsi, Amali ya kula shi ya kai masa waƙa. 

 

    G/Waƙa : Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun  Za ni wurin

: Kiɗi.

 

   Jagora: In dai da dama,

: Dama dawo[1] akai,

   ‘Y/Amshi: In babu dama sai a yi dangana,

: Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun  za ni wurin

: Kiɗi.

 

 Jagora: Ku ɗan rage mani in hwaɗi mai : dawo,

 ‘Y/Amshi: Ku ɗan rage mani,

 : In hwaɗi mai dawo,

 

 Jagora: Ina dawon yake?

: Ina dawon yake?

     ‘Y/Amshi: Ina dawon yake?

: ‘Yammani in ƙuta[2].

   : Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun,

: Za ni wurin kiɗi.

 

Jagora: In dai ana dara hid da uwa akai.  ‘Y/Amshi: Lalle irin haka gane maza akai,

 

Jagora: In dai ana haka,

: Gane maza mukai,

 ‘Y/Amshi: Lalle irin haka,

: Gane maza mukai,

: Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.

 

Jagora: Ku na Arewa,

: Da ku da na nan kudu,

   : Na Yamma,

: Da ku jama’ag Gabas,

   : Maza da mata kui mani gahwara.

‘Y/Amshi: Amali gobe gida yaka son zuwa.

: Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.

 

     Jagora: Abdu Karimun,

: Abdu Karimun,

‘Y/Amshi: Hatta[3] tahiyakka,

: Kama da ta Rabi’u.

 

     Jagora: Ko maganakka,

: Kama da ta Rabi’u,

‘Y/Amshi: Ko maganakka,

: Kama da ta Rabi’u.

   : Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.

 

 Jagora: Masu zuwa haji kui ta zuwa haji,

 ‘Y/Amshi: In don karen ɓuki[4],

: Ba ya zuwa haji,

   : Sai dai ya sami gyaɗa,

: Ya yi ƙanƙara,

   : Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.

 

Jagora: Ina Kulun take?

: Hauwa Kulun Kulu,

 ‘Y/Amshi: Hauwa Kulun Kulu,

: Ke gwadi kin aje[5],

: Da ke da Dammo,

: Kui mani : taimaka,

: Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.

 

Jagora: Masu zuwa haji kui ta zuwa haji,

‘Y/Amshi: In dan karen ɓuki,

: Ba ya zuwa haji,

   : Sai dai ya sami gyaɗa,

: Ya yi ƙanƙara,

   : Ko da rani ba ya zama gida,

: Gidan Karimun za ni wurin kiɗi.



[1]  Gayan fura

[2]  A ɗebi kaɗan a ci don a ji daɗinsa ko kyawonsa.

[3]  Ko/har ma.

[4]  Dila sarkin dubara.

[5]  Samun zarafi/hal/dukiya.

Post a Comment

0 Comments