Ticker

6/recent/ticker-posts

Salau Na Maimuna

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Salau Na Maimuna

Salau na Maimuna mutumen garin Ma’azawa ne, riƙon Batamna a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Noma ne aikinsa don har ya yi bukin dubu, Amali ya yi masa waƙar ne saboda shaharar tasa.

 

G/Waƙa : Wuce maza bisa noma,

: Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

 

      Jagora: Wuce maza bisa noma,

: Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

     ‘Y/Amshi: Wuce maza bisa noma,

   : Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

 

    Jagora: Salau na Maimuna,

    ‘Y/Amshi: Allah ya hore ma aiki.

 

    Jagora: Mijin Damore da Tcito,

    ‘Y/Amshi: Zango[1] zaɓen Allah.

 

     Jagora: Mijin Damore da Tcito.

      ‘Y/Amshi: Zango zaɓen Allah.

 

   Jagora: Wani miki ya warke,

   ‘Y/Amshi: Wani miki[2] ta tashi.

 

   Jagora: Wani Anne ya kwanta.x2

   ‘Y/Amshi: Wani Anne ya tashi.x2

 

   Jagora: Su wane ba su da aiki,

   ‘Y/Amshi: Sai dai kabrab bashi.

: Wuce maza bisa noma,

   : Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

 

   Jagora: Ku dai jiddun[3] bashi,

   : Ku dai jiddun bashi,

   ‘Y/Amshi: Sai bashi ya ci ku.

   : Wuce maza bisa noma,

   : Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

 

   Jagora: An sai ragon suna,

   : An koma an sai sa,

: Kuma dai ba ko sisi,

: Hag geron an iba,

: Kuma dai ba ko ahu[4].

   ‘Y/Amshi: Goɗiya aka dubi,

: Ta kai jikka ukku.

: Wuce maza bisa noma,

   : Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

 

   Jagora: Gona ce nis shikke,

   : Yad duƙa yan nome,

   : Nik koma wajjen can,

   : Ni iba nis sara,

   : Yad duƙa yan nome,

   : Nik koma wajjen nan,

   : Ni iba nis sara,

   : Yak koma yan nome.

   ‘Y/Amshi: Abin da kai mani,

: Aikin noma bai kai can ba.

: Wuce maza bisa noma,

   : Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.

 

   Jagora: Kulkin horon jema,

   : Na Sada ka yi ma aikin,

   : Gona shiɗam maiki.

   ‘Y/Amshi: Wuce maza bisa noma,

   : Kulkin horon jema,

: Na Sada ka yi ma aikin,

: Gona jiɗam maiki.



[1]  Wani irin gero ne mai doguwar zngarniya.

[2]  Ciwo/ rauni.

[3]  Koyaushe.

[4]  Kwabo da ɗari kenan, abin nufi dai ba a biya kuɗI ba.

Post a Comment

0 Comments