Mai Galmak Kashin Haki Isah

    Citation: Bungudu, H. U. (2023). ZaÉ“aÉ“É“un waÆ™oÆ™in mawaÆ™an baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bungudu
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Noma

    Mai Galmak Kashin Haki Isah

     

    G/Waƙa: Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     

    Jagora: Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     ‘Y/ Amshi: Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     

     Jagora: Gidan Hamma za ni na.

    ‘Y/ Amshi: In kwance takaici ban rammai,

    : Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     

     Jagora: Yaro gahwarakka ga

     ‘Y/ Amshi: Manya

    : Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     

      Jagora: Ni dole in yi ma kiÉ—i,

    ‘Y/ Amshi: Ai shikka a zan tar da gero.

     

    Jagora: Tilas in yi maka kiÉ—i

     ‘Y/ Amshi: Don ko ya bi baya jin rana.

     

      Jagora: Wandara ka biya kiÉ—i,x2

    ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya Æ™ara mai girma.x2

     

    Jagora: Abul azizu ka biya,

     ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya Æ™ara mai girma

     

      Jagora: Gidan Hamma za ni na,

    ‘Y/ Amshi: Domin su ka son kiÉ—in noma.

    : Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     

    Jagora: Ni dai abin da nig gani,

     ‘Y/ Amshi: Kyan ÆŠanÉ—a ya gadi babanaix2.

     

      Jagora: Kowag gadi arziki,

    ‘Y/ Amshi: Sai ya yi shi duniya daidai.

     

    Jagora: Gero na gidanka Isah,

     ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

      Jagora: Dawa na gidanka Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

      Jagora: Maiwa na gidanka Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

      Jagora: Masara na gidanka Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

    Jagora: Shinkahwa na gidanka Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

    Jagora: Wake na gidanka Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

     Jagora: Gujiya na gidanka Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

     Jagora: KuÉ—É—i gas u nan ga Isah,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho yana cisai.

     

    Jagora: Abul azizu ya biya,x2

    ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya Æ™ara mai girma,x2

     

    Jagora: Na gode ma Madugu,

     ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya Æ™ara mai girma

    : Ya yi an gani,

    : Mai galmak kashin haki Isah.

     

     Jagora: Wandara ka biya kiÉ—i,

     ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya Æ™ara mai girma,x2

     Jagora: Kun ga Magaji sarki na,

     ‘Y/ Amshi: Wata’ala ya Æ™ara mai girma,x2

     

     Jagora: Gidan Hamma ba Bahili,

     ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho suna cisai.

     

      Jagora: Kwatarmawa akwai maza,

    ‘Y/ Amshi: Yau kowat taho suna cisai.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.