Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Jikan Barmo
G/Waƙa: Yaro Wanda As Shiryayye.
Jagora: Aiki ya hirgice É—an Musa,
: Jikan Barmo maza manoma,
: Mai wa gona shigar gayya.
‘Y/Amshi : Dan ka taso aikin ka noma,
: Aiki in ya buwaya sai su,
: Don ka taso aikin manoma,
: Aiki in ya buwaya sai shi.
Jagora : Aiki ba za ya ƙarewa ba,
: In ba dan soja anka kai rai ba,
: Yaƙi ba za ya ƙare
wa ba,
: In ba É—an
soja anka kai rai ba.
‘Y/ Amshi : Aiki ya hirgice É—an
musa ,
: Jikan barmo maza manoma,
: Mai tsoron zuciyar uba,
: Sannan shi ba ya batu nai,
Jagora : In dai nauyin buhu guda,
: Ba ya kashe jaki da adda ƙarhi,
: Bayan dai nauyin buhu guda,
: Baya kashe jaki da adda ƙarhi,
: Yaro ne wanda as shiryayye,
: Gaba dai gaba dai É—an Musa,
: Ga tsoron zuciyar uba,
: Sannan shi baya tsallake batu nai.
‘Y/ Amshi : Aiki ya hirgice É—an
Musa,
: Yaro ba dai yakai garai ba,
: Ko ya anka shinhiÉ—a mai,
: Kai yaro ba zai kai ga rai ba,
: Ko ya anka shinhiÉ—a mai,
: Musa in ya kama noma,
: Kafin ya cimma ka,
: Ni ya zata taki sanin dawowa tai da
sahe,
: Ya take sawun kura,
: In an kai bayan mangariba,
: Ita kura ta take sani nai,
: Aiki ya hirgice ÆŠan Musa,
: Jikan Barmo maza manoma,
: Mai ma gona shurin gaba,
: Yaro ne wanda ar shiryayye,
Jagora : Tsoho ya bar biÉ—ar budurwa,
: In ba dogon kwaÉ—ai garai ba,
: Tsoho yabar biÉ—ar budurwa,
: In ba dogon kwaÉ—ai garai ba,
: Tsoho yabar biÉ—ar budurwa,
: Ko in ya biÉ—e[1]
ta hira,
: In har taso ta tsugunna shi,
: Da ta zo sai ta durƙusa mai,
: Ta ce mai yaushe kaz zo.
‘Y/ Amshi : Aiki ya hirgice É—an
Musa,
: Jikan Barmo maza manoma,
: Mai ma gona shuwen gaba,
: Yaro ne wanda as shiryayye.
Jagora:
Ya ce aiko su aka yi,
: Sai ya ce ba aiko shi aka yi ba,
: Ya ce aiko shi aka yi,
: Sai ya ce ba aiko shi aka yi ba,
: Ya ce mai ɗan karen taɓaɓɓe[2],
: Ya ce mata yar karan taɓaɓɓe,
: Ki bamu kuÉ—in da munka bayar,
: In ba kuÉ—in ubanki ne ba.
‘Y/
Amshi: Aiki ya hirgice É—an Musa,
: Jikan Barmo maza manoma,
: Mai ma gona shigar gayya,
: Yaro ne wanda as shiryayye.
Jagora : Yaro ne wanda ar
shiryayye,
: Gaba dai gaba dai gaba É—an Musa,
: Ga tsoron zuciyar uba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.