Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ma’anar Salo
Malamai da masu nazarin adabi sun bayar da ma’anar salo
ta hanyoyi da dama duk da yake kusan manufa ɗaya suka fuskanta, kalmomin da suka yi amfani da su kawai
ka bambanta.
“Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce wadda makaɗi ke kyautata zaren tunaninsa, ya sarrafa shi cikin azanci don ya cim ma
burinsa na isar da saƙo a waƙa”. Gusau (2003:54).
Ga abin da
wanna masani ya nuna salo shi ne dabarun da mai magana ya ƙunsa a cikin zancensa
da nufin isar da saƙo ta hanyar da za a fahimce shi cikin sauƙi ko da wahala, a
cikin raha ko cikin ƙosawa. Duk ta hanyar da masu saurare suka ji jawabin daga hanyoyin da aka
ambata, to shi ne irin salon da mai zancen ya yi amfani da shi.
A wata
ma’anar da aka bayar cewa aka yi:
“Salo yana
nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda
aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan
dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta
yadda saƙon waƙar zai isa ga
mai saurare ko karatun waƙar” Yahya
(1999:3).
Wanna ma’ana ita ma kusan
manufarta ɗaya da
wadda ta gabace ta. Bayani yana nuni ne ga iri dabarun da mawaƙi yake amfani da su wajen isar da saƙonsa ga jama’a a cikinsa ba tare da gundura ba. Wato saƙonsa ya isa cikin birnin zuciyar masu saurare cikin nishaɗi da ban sha’awa.
Shi kuma wani malamin cewa ya yi:
“Masana da manazarta suna ganin cewa salo yana da wuyar a gane shi a bisa kansa sai dai ana iya gane wasu sigogi nasa dangane da ma’anarsa.To amma muna iya cewa salo shi ne hanyoyin isar da saƙo” Ɗangambo (2007:34)
Bayanin wanna malami bai tsawaita ba. Ya taƙaita abin da waɗanda aka fara ambata suka faɗa tare da ƙara bayyana wahalar bayyana ma’anar salo ta amfani da kalmomi kawai. Duk da haka ya taƙaita ya ce hanyoyin isar da saƙo su ne salo, waɗanda nake ganinn su ne waɗanda waɗancan malamai da na fara ambata suka faɗa.
A bisa bayanan masana ana iya
cewa, salo wata dabara ce ta isar da saƙo ta
hanyar zaɓen
kalmomin da suka dace da abinda ake zance ta yada zuciyar mai saurare ko
karatun abun zai ta karɓe shi
ya Allah a cikin sauƙi ko tsauri.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.