Ticker

6/recent/ticker-posts

Lauwali Matusgi

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Lauwali Matusgi

 

G/Waƙa: Gona yak kwan yana kashin,

: Alkamat turwa[1]

: Zaki ko gobe ba ka tso,

: Ron hakin gona.

 

Jagora: Sai na bi Matuzgi,

: In tsaya in gaida mazajena.x2

‘Y/ Amshi: Sun aje damman daka,

: Suna taimakak kowa.x2

 

Jagora:Sun aje

‘Y/ Amshi: Damman daka suna taimakak kowa.

 

Jagora: Lauwali zaki.x2

‘Y/ Amshi: Ko hwari akai,

: Bai yini birni.x2

: Gona yak kwan yana kashin,

: Alkamat turwa.

 

Jagora: Da kai aka dibin kashin haki,

‘Y/ Amshi: In ji gangammu

: Yanzu a ƙare shi mai kiɗi,

: In shige birni.

Jagora: Lauwali zaki

‘Y/ Amshi: Ko hwari akai,

: Bai yini birni.

: Gona yak kwan yana kashin,

: Alkamat turwa.

 

Jagora: Ka ji kiɗin noma,x2

.’Y/ Amshi: Wanda bamu wa,

: Wani masganab banza.x2

: Gona yak kwan yana kashin,

: Alkamat turwa.

 

Jagora: Alhaji Mamman Hubbare na yaba.,

‘Y/ Amshi: Ban rena kyauta ba

: Tabaraka Allah ya ƙara mai,

: Ba karo komi.

 

Jagora: Alhaji Mamman

‘Y/ Amshi: Hubbare na yaba ya yi alheri,

.: Tabaraka Allah ya ƙara mai,

: Ba karo kuɗɗi

.

Jagora: Baba na gode.

‘Y/ Amshi: Iro Duniya,

: Don ga kari yai man

.

Jagora: Na gode

‘Y/ Amshi: Iro Duniya,

: Don ga kari yai man

: Tabaraka Allah ya ƙara mai,

: Ba karo kuɗɗi.

Jagora:Da ya ji kalamin kashin haki,

‘Y/ Amshi: Wasa mai noma

 

Jagora: Ya yi kalamin kiɗinmu mai,

‘Y/ Amshi: Wasa mai noma.

: Gona yak kwan yana kashin,

: Alkamat turwa.

 

Jagora: Ƙara ƙari ragi suna inda Maiƙaura,

‘Y/ Amshi: Ummaru duw wanda ba kwabo,

: Bai zuwa ƙara.

 

Jagora: Ƙara ƙari rashin ragi

‘Y/ Amshi: Ba Karin sahe

: Maikiɗi sunansu bai shige,

: Man ga raina ba.

 

Jagora: Mai kiɗi.

‘Y/ Amshi: Sunansu bai shige man ga raina ba,

 

Jagora: Sai na bi ta hubbare.

: In tsaya in garza mazajena.

‘Y/ Amshi: Sun aje damman daka suna,

: Taimakak kowa.

 

Jagora: In bi ta hubbare

‘Y/ Amshi: In yi ro,

: Ƙo ga rabbani

: Mu samu ganin ya Rasulu da,

: Hamdala ta yi.

 

Jagora: Mu samu,

 ‘Y/ Amshi: Ganin ya Rasulu da,

: Hamdala ta yi.

: Gona yak kwan yana kashin,

: Alkamat turwa.



[1]  Haki ne ko ciyawa wadda manoma ke nomewa a gonarsu.

Post a Comment

0 Comments