Ticker

6/recent/ticker-posts

Haruna

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Haruna

 

G/Waƙa: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

 

Jagora: Gidan Haruna,

: Za ni yo kiɗina,

: Mai kai dare..,

  ‘Y/ Amshi: Mai kai dare daji,

: Baya tadda[1] kainai.

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

  Jagora: Amman na zaɓi mai iko,

: Korau ɗiyan manoma,

: In damana ta komo

: Ku kama hauya,

: Kun san rayuwa,

: Rannan ba zama akai ba,

: In ana noma,

: Ba zama akai ba.

: Rannan mai zaman saƙa,

: Shina wahalsa  kainai,

: Kuma mai hwarauta,

: Ba sassabe[2] yakai ba,

: Rannan mai zaman dara,

: Wannan ba shi fara binne

: To maza ku ɗau kalme,

: Ko kuɗauki kwasa,

: Kui sassabe daji,

: Kui kashe kalage,

: To ɗan da bai da dame,

: Mace ba ta so nai

‘Y/ Amshi: Bai da dame[3],

: Macce ba ta so nai.

 

 Jagora: To ɗan da bai da hura,

‘Y/ Amshi: Macce bata so nai.

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

 

 Jagora: Ka san kowal aje,

: Mata baabin dakawa,

: Kun san shina cikin wahala,

: Ta zakkona ishe mai.

: Ko can batun Allah,

 ‘Y/ Amshi: Ko can batun Allah,

: Babu mai hanawa.

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

 

 Jagora: Sannan Arabazan ko,

: Mawa can na tana nan,

: Ka san Haruna na gode.

: Garba yamiƙa min.

: Don ya bada ingarma,

: Tungar mai hwarin ƙahwahu

: Sannan Gidan kuru,

: Zan sauka Haruna na nan.

: Shi Haruna nagode,

: Ya biya kiɗina.

: Sannan zani na Zango,

: In gano manoma,

: Allah shi bar Labaran,

: Mai halin yabawa,

: Allah..

‘Y/ Amshi: Ya hi mu yaba

: Wa ya bam mu tare,

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

 Jagora: Sannan ka hwaɗa ma raggo,

: Bana bai

: San halin Rugum ba,

: Don kun ga ‘yan makaɗa,

: Sai ku ce Rugum na,

: Kuma had da masu duma,

: Had da mai kalangu,

: Dud dai inda sun yi kiɗi,

: Sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Kotso

: Sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Taushi sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Ganga

: Sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Goge sai a ce Rugum na.

: Mai gunduwa[4] ka kiɗi,

: Sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Kwamsa sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Gora sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Goge sai a ce Rugum na,

: Kuma had da mai,

: Kuntugi

: Sai a ce Rugum na,

: Ka san ni ar Rugum,

: Da gani babu tambaya ba,

: Ka san ni ar Rugum,

: Yarana Rugum suna nan,

: Kun san karonmu sai manya,

: Sai gidan saraki[5],

: To ɗan da..

  ‘Y/Amshi: Ɗan da yad dace,

: Bisa duniyag ga,x2

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

 

 Jagora: Amma ni zan kiɗi Gumi,

: Don in gano manoma,

: Ka san Bello na gode,

: Ya biya kiɗina,

: Ɗan noma mai abin noma,

: Shina da kyuta,

: Dub Bello Ɗan Jabiri,

: Ya biya kiɗina,

: Dub Bello mai,

: Gona wadda ba irin ta,

: Sannan ni zan Tsarna,

: Za ni sauka,

: Tsarnawa na yi kiɗi,

: Don Haruna na nan,

: Ka san Haruna shid[6] da gida,

: Wanda ba iri nai.

: Allahx2

‘Y/ Amshi: Allah ya hi mu yabawa,

: Ya bar nu tare,x2

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.

Jagora: Dan nan Debetu zan,

: Koma wa Ɗanladi na can,

: Ka san Ɗanladi na gode,

: Ya biya kiɗina,

: Amma Ma’azu na gode,

: Shi ya biya kiɗina,

: Dan nan Turanki zan,

: Koma wa gidan manoma,

: In na ga Ɗan’indo,

: Bani shan takaici[7],

: Allah,

‘Y/ Amshi: Ya ƙara yabawa,

: Ya bam mu tare,

: Yai halin girma,

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi manoma,

: Biɗan na kainai.

 

 Jagora: Amma maza inai maku,

: Horo ɗiyan manoma,

: Ka san ni yadda ba ni kiɗi,

: Sai kiɗin manoma,

: Amma kiɗin hura,

: Mai daɗi ga ‘yan manoma.

: Amma ga wanda ya aje,

: Gero cikin rihenu[8],

: Amma ka hwaɗa ma raggo,

: To bana sai,

: Ya ji ƙwal ga kainai,

: To ɗan Karen shege,

: Ba mu ba ka kyauta,

: Yai halin girma[9],

: Yai halin yabawa,

: Haruna ya hi mano,

: Ma biɗan na kainai.



[1]  Kulawa ko damuwa, ma’ana dai hankalinsa a kwance..

[2]  Gyara gona ta hanyar sassare kututturai da tottohi.

[3]  Daurin hatsi wanda ake ɗaurawa idan za a ɗauko daga gona zuwa gida.

[4]  Wata ‘yar ganga ce da ake kiɗin nomad a ita wadda ba ta kai girman gangar noma ba.

[5]  Masu sarauta.

[6]  Shi ke da.

[7]  Haushi/jin kunya.

[8]  Rumbuna.

[9]  Kyauta/kyautatawa.

Post a Comment

0 Comments