Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhaji Dangwaggo

Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Alhaji Ɗangwaggo

 

 G/Waƙa: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar aiki.

Jagora: Alhaji buzu koma shirin noma

‘Y/ Amshi: Alhaji buzu mai rigimar aiki.

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar aiki.

 

Jagora: Abdukarimun na gode

‘Y/ Amshi: Allah ya ƙara girman

: Mai mana alheri

 

  Jagora: Na gode malan Abdulkarimun na gode,

‘Y/ Amshi: Wata’ala ya ƙara girman mai mana alheri.

: Yai murna da kiɗin Daudu

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar[1] aiki.

Jagora: Jawo ruwa ga noma Alhaji,

‘Y/ Amshi: Jawo ruwa ga noma

: Alhaji Ɗangwaggo.

.

  Jagora: Alhaji jikan

‘Y/ Amshi: Ummaru mai geza.

: Ya saba da yini daji

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar aiki.

.

Jagora: Shugaban manoman ƙasam Maradun.x2

‘Y/ Amshi: Alhaji kai anka naɗa

: Mai hanƙuri da adalci

: Da nuhin hairi.x2

 

Jagora: Alhaji ya yi dubun damman

: Ya yi dubun damman dawa,

‘Y/ Amshi: Kullun tuwo akai gidanai,

: Kullun hura akai gidanai,

: Ya bar jin samatay[2] yunwa.

 

Jagora: Alhaji,

‘Y/ Amshi: Ya baj jin samatay yunwa.

 

Jagora: Da gaskiya da ƙarya.x2

‘Y/ Amshi: Ba su zama ɗai,

: Mun leƙe ƙarya ba magana ce ba.x2

 

Jagora: Baba ka sai mota ka yi mani Honda.x2

‘Y/ Amshi: In hau in gwadi rinjaya,

: In tcere ma na Mologo.x2

 

Jagora: Dogo na Salau barka.

‘Y/ Amshi: Na Salau barka da kashin gamba.

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai mai rigimar aiki.

  Jagora: Alhaji buzu koma shirin noma.

‘Y/ Amshi: Alhaji dud da irinsu manomanmu.

 

Jagora: Alhaji buzu mai jaraban noma

‘Y/ Amshi: Alhaji dud da irinsu manomanmu.

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar aiki.

 

Jagora: Na sarkin Kano koma gona.x2

‘Y/ Amshi: Alhaji kar ka sake gwadi rinjaya.x2

 

Jagora: Alhaji ga sana’ar tebur

: Ya je Legas ya yi Shagamu

 ‘Y/ Amshi: Alhaji in ya taho gida Janbaƙo yana daji.

.: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar aiki.

 

Jagora: Alhaji yai gona Hwaru

: Alhaji yai gona Magami

: Alhaji yai gona Tudun garka.

: Alhaji yai gona Maradun

: Alhaji yai gona Mahwara.

‘Y/ Amshi: Alhaji yai gona Mahwara.

: Ka zan mai rigimar aiki.

 

Jagora: Alhaji,

‘Y/ Amshi: Ka zan mai rigimar aiki.

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai mai rigimar aiki.

Jagora: Jawo ruwa ga noma,

‘Y/ Amshi: Jawo ruwa ga noma.

: Mai rigimar aiki.

: Ya saba da yini daji

: Mu gaisai,

: Mai rigimar aiki.[1]  Mai cika aiki da yawa.

[2]  Alamun/faruwar wani abu kaɗan.

Post a Comment

0 Comments