Wata rana Shehu Jaha yana saran reshen bishiya da gatarinsa, sai ya zauna a can saman reshen da yake sarewa. Sannan wurin da yake saran na gefen da ke tsakaninsa da bishiyan. Wato dai yana zaune a wurin da idan an sare zai rabu da bishiyar.
Can sai ga wani malami ya zo wucewa. Malami ya dubi Shehu Jaha ya ce: "Kai kuwa bawan Allah ta yaya za ka yi haka?"
Shehu Jaha ya ce: "Me fa na yi?"
Malami ya ce: "Ai idan ka sare reshen nan to kai ma faÉ—uwa za ka yi."
Shehu Jaha: "Ka san gaibu ne?"
...
Da malami ya ga Shehu Jaha zai É“ata masa lokaci, sai ya kaÉ—a rigarsa ya yi gaba yana cewa: "Mai rabon shan duka..."
Shehu Jaha na ƙara sare reshe sai ga shi sun yi kasa tare ricaaaa!
Bayan Shehu ya yi ɗan noƙe-noƙe jin zafi, sai ya ce: "Lallai duk yadda aka yi malamin nan da wuce waliyi ne, kuma ya san gaibu." Bai yi wata-wata ba sai ya bi bayansa da gudu. Ina iske shi ya sha gabansa yana faɗin: "Wallahi tun da ka san gaibu, sai ka sanar da ni ranar da zan mutu."
Malamin ya yi ta ƙoƙarin fahimtar da Shehu Jaha cewa babu wanda ya san gaibu sai Allah, amma Shehu bai sarara ba. Da malam ya ga alamar kamar motsi ne, sai ya ce masa: "To duk ranar da jakinka ya yi kuka sau uku a jere, ranar ce za ka mutu."
Shehu Jaha jaha ya rabu da malami ya taho gida cike da zulumi.
Washe gari yana zaune sai jakinsa ya yi kuka. Nan fa cikinsa ya ɗuri ruwa. Ba a jima ba kuwa ya sake kuka. Nan Shehu Jaha ya nufi wurin jaki a guje yana ba shi haƙuri. Can kuwa jakiki ya yi kuka na uku. Nan Shehu Jaha ya kwanta ya mimmiƙe wai shi ya mutu.
Can matar Shehu Jaha da ke ta jiran ya zo ya ba ta kuɗin cefane ta ga shirun ya yi yawa. Ta garzayo ta wurin turken jaki sai ga Shehu Jaha a mimmiƙe. Ta ce: "Shehu in ce dai lafiya? Ni da nake jiran kuɗin cefane?"
Shehu Jaha ya ta da kai ya ce: "Da ina da rai kin dame ni kan kuÉ—in cefane. Yanzu da na mutu ai kina shafini lafiya!"
...
Matar Shehu Jaha ta yi waje don kiran abokinsa a maƙwabta.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.