Ticker

6/recent/ticker-posts

Karmanje Kanen Bawa

 Citation: Bungudu, H. U. (2023). Zaɓaɓɓun waƙoƙin mawaƙan baka na noma. Ahmadu Bello University Press Ltd.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bungudu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Noma

Ƙarmanje Ƙanen Bawa

 

  G/Waƙa: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.

 

  Jagora: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.

  ‘Y/Amshi: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.

 

 Jagora: Baban Hauwa da Garba,

: Ƙanen Muhammadu,

: Ka ji mazan yaƙi,

‘Y/ Amshi: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.

 

  Jagora: Kaji sun ƙare sun bar ass[1], x2

‘Y/ Amshi: Na gano zancen banza.x2

: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.

 

Jagora: Buƙe da Rubduge,

: Da ƙiri-ƙiri,

‘Y/ Amshi: Had da Allah waddai,

: Sun tsaya wuri guda daji,

: Ba su ƙulla aikin komi ba.

: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.

 

Jagora: Ƙarmanje na da sa’ar  aure,

: Bai biɗar ɗiyar mai ƙyamushe.

: Mai biɗaɗ ɗiyam ma gaye,

: Kul ba ya koma ƙumaji,

‘Y/ Amshi: Yana taƙama ɗage sutura,

: Ɗaiwajje[2].

: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a barma aiki,

: Ƙarmanje.

 

 Jagora: Ma tihwa ya sai[3] nama,

: Ya ba matatai ta dahwa,

: Nan kau naman ya nina,

: Ta ɗau tulu tai ruwa,

: Yaɗ ɗau naman ya canye,

: Tad dawo tat tambaya,

: Tac ce wat taɓa naman ga?

: In ni nac ci namanga,

: Sai a yi man hadarin kaina,

: Kahin a jima sai yaj ji cida,

: Ga hadari ya kama,

: Kamin a jima sai ya ji,

: Daɗin Allah ba a yi mai  ɓoyo,

‘Y/ Amshi: Mutum aka wa gezaji[4],

 

Jagora : Allah baa yi mai  ɓoyo,

‘Y/ Amshi: Mutum aka wa gezaji,

: Yag gane sai ya ɓoye,

: Ya fito yana kuka,

: Yana ta faɗin

: Na tuba,

: Ɗan kaɗan na ɗiba,

: Na tuba.

: Ƙanen  Bawa,

: Mai kuge a bar ma aiki,

: Ƙarmanje.x2



[1]  Yadda Hausawa suke faɗi idan za su kori kaji.

[2]  Gefe ɗaya.

[3]  Sayi/saye/siya.

[4]  Ɓoye-ɓoye.

Post a Comment

0 Comments